1
W.Yah 19:7
Littafi Mai Tsarki
HAU
Mu yi ta murna da farin ciki matuƙa, Mu kuma ɗaukaka shi, Domin bikin Ɗan Ragon nan ya zo, Amaryarsa kuma ta kintsa.
Compare
Explore W.Yah 19:7
2
W.Yah 19:16
Da wani suna a rubuce a jikin rigarsa, har daidai cinyarsa, wato Sarkin sarakuna, Ubangijin iyayengiji.
Explore W.Yah 19:16
3
W.Yah 19:11
Sai na ga sama ta dāre, sai ga wani farin doki! Mahayinsa kuwa ana ce da shi Amintacce, Mai Gaskiya, yana hukunci da adalci, yana kuma yaƙi.
Explore W.Yah 19:11
4
W.Yah 19:12-13
Idanunsa kamar harshen wuta suke, kansa da kambi da yawa, yana kuma da wani suna a rubuce, wanda ba wanda ya sani sai shi. Yana saye da riga wadda aka tsoma a jini, sunan da ake kiransa da shi kuma, shi ne Kalman Allah.
Explore W.Yah 19:12-13
5
W.Yah 19:15
Daga cikin bakinsa wani kakkaifan takobi yake fitowa, wanda zai sare al'ummai da shi, zai kuwa mallake su da tsanani ƙwarai, zai tattake mamatsar inabi, ta tsananin fushin Allah Maɗaukaki.
Explore W.Yah 19:15
6
W.Yah 19:20
Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.
Explore W.Yah 19:20