1
W.Yah 21:4
Littafi Mai Tsarki
HAU
zai share musu dukkan hawaye. Ba kuma sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba, don abubuwan dā sun wuce.”
Compare
Explore W.Yah 21:4
2
W.Yah 21:5
Sai na zaune a kan kursiyin ya ce, “Kun ga, ina yin kome sabo.” Ya kuma ce, “Rubuta wannan, domin maganar nan tabbatacciya ce, gaskiya ce kuma.”
Explore W.Yah 21:5
3
W.Yah 21:3
Na kuma ji wata murya mai ƙara daga kursiyin, tana cewa, “Kun ga, mazaunin Allah na tare da mutane. Zai zauna tare da su, za su zama jama'arsa, Allah kuma shi kansa zai kasance tare da su
Explore W.Yah 21:3
4
W.Yah 21:6
Sai ya ce mini, “An gama! Ni ne Alfa, Ni ne Omega, Ni ne na Farko, Ni ne kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi ruwa daga maɓuɓɓugar ruwan rai kyauta.
Explore W.Yah 21:6
5
W.Yah 21:7
Duk wanda ya ci nasara, zai ci wannan gādo, wato, in zama Allahnsa, shi kuma ya zama ɗa a gare ni.
Explore W.Yah 21:7
6
W.Yah 21:8
Amma matsorata, da marasa riƙon amana, da masu aikin ƙyama, da masu kisankai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk maƙaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai cin wuta da kibiritu, wanda yake shi ne mutuwa ta biyu.”
Explore W.Yah 21:8
7
W.Yah 21:1
Sa'an nan na ga sabuwar sama da sabuwar ƙasa, don sama ta farko da ƙasa ta farko sun shuɗe, ba kuma sauran teku.
Explore W.Yah 21:1
8
W.Yah 21:2
Sai na ga tsattsarkan birni kuma, Sabuwar Urushalima, tana saukowa daga Sama daga wurin Allah, shiryayyiya kamar amaryar da ta yi ado saboda mijinta.
Explore W.Yah 21:2
9
W.Yah 21:23-24
Birnin kuwa ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, domin ɗaukakar Allah ita ce haskensa, Ɗan Ragon kuma fitilarsa. Da haskensa al'ummai za su yi tafiya. Sarakunan duniya za su kawo darajarsu a gare shi.
Explore W.Yah 21:23-24