1
Zab 5:12
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ka sa wa masu yi maka biyayya albarka, ya Ubangiji, Alherinka yana kāre su kamar gārkuwa.
Compare
Explore Zab 5:12
2
Zab 5:3
A gare ka zan yi addu'a, ya Ubangiji, Da safe za ka ji muryata, Da hantsi zan yi addu'ata, In kuma jira amsa.
Explore Zab 5:3
3
Zab 5:11
Duk waɗanda suka fake gare ka za su yi farin ciki, Kullum za su yi ta raira waƙa domin murna. Kana kiyaye waɗanda suke ƙaunarka, Suna kuwa matuƙar murna saboda kai.
Explore Zab 5:11
4
Zab 5:8
Ina da abokan gāba da yawa, ya Ubangiji, Ka bi da ni in aikata nufinka, Ka kuma fayyace mini hanyarka domin in bi ta!
Explore Zab 5:8
5
Zab 5:2
Ya Sarkina, Allahna, Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako.
Explore Zab 5:2