1
Josh 6:2
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Duba, na ba da Yariko, da sarkinta, da jarumawanta a hannunka.
Compare
Explore Josh 6:2
2
Josh 6:5
Sa'ad da suka tsawaita busar ƙahoni, sai dukan jama'a su yi ihu da babbar murya, garun birnin kuwa zai rushe tun daga tushensa. Sai mutane su haura, ko wanne ya nufi inda ya fuskanta sosai zuwa cikin birnin.”
Explore Josh 6:5
3
Josh 6:3
Kai da dukan mayaƙa za ku zagaya birnin sau ɗaya kowace rana har kwana shida.
Explore Josh 6:3
4
Josh 6:4
Sai firistoci bakwai su riƙe ƙahonin raguna a gaban akwatin alkawari. Amma a rana ta bakwai za ku zaga birnin sau bakwai, firistoci su yi ta busar ƙahoni.
Explore Josh 6:4
5
Josh 6:1
Aka rufe Yariko ciki da waje, ba mai fita, ba mai shiga saboda Isra'ilawa.
Explore Josh 6:1
6
Josh 6:16
A zagawa ta bakwai, sa'ad da firistoci suka busa ƙahoni, sai Joshuwa ya ce wa jama'a, “Ku yi ihu, gama Ubangiji ya ba ku birnin.
Explore Josh 6:16
7
Josh 6:17
Amma birnin da dukan abin da yake cikinsa haram ne ga Ubangiji, sai a hallaka su. Rahab karuwan nan kaɗai ce, da dukan waɗanda suke tare da ita a gidanta za a bari da rai domin ta ɓoye 'yan leƙen asirin ƙasa da muka aika.
Explore Josh 6:17