1
Ish 65:24
Littafi Mai Tsarki
HAU
Zan amsa addu'o'insu tun ma kafin su gama yin addu'a gare ni.
Compare
Explore Ish 65:24
2
Ish 65:17
Ubangiji ya ce, “Ina yin sabuwar duniya da sabon sararin sama. Abubuwa na dā za a manta da su ɗungum.
Explore Ish 65:17
3
Ish 65:23
Aikin da suka yi zai yi nasara, 'ya'yansu ba za su gamu da bala'i ba, zan sa musu albarka duk da zuriyarsu har dukan zamanai.
Explore Ish 65:23
4
Ish 65:21-22
Mutane za su gina gidaje su kuwa zauna a cikinsu, ba waɗansu dabam za su mori gidajen ba. Za su dasa gonakin inabi su kuwa ji daɗin ruwan inabi, ba waɗansu dabam za su sha shi ba. Mutanena za su yi tsawon rai kamar itatuwa. Za su ci cikakkiyar moriyar abubuwan da suka yi aikinsu.
Explore Ish 65:21-22
5
Ish 65:20
Jarirai ba za su mutu tun suna jarirai ba, ko wanne zai cika yawan kwanakinsa kafin ya mutu. Waɗanda suke masu shekara ɗari da haihuwa su ne samari. Waɗanda suka mutu kafin wannan lokaci, to, alama ce, ta cewa na hukunta su.
Explore Ish 65:20
6
Ish 65:25
Kyarketai da 'yan raguna za su ci abinci tare, zaki kuma zai ci budu kamar yadda shanu suke yi. Maciji ba zai ƙara zama abu mai hatsari ba. A kan Sihiyona tsattsarkan dutsena, ba za a sami wani abu da zai cutar ba, ko wani mugun abu.”
Explore Ish 65:25
7
Ish 65:19
Ni kaina kuma zan cika da murna saboda Urushalima da jama'arta. Ba kuka a can, ba bukatar neman taimako.
Explore Ish 65:19
Home
Bible
Plans
Videos