Ba za a ƙara ce da ke, “Yasasshiya” ba,
Ko a ce da ƙasarki, “Mata wadda Mijinta ya Rabu da Ita.”
Sabon sunanki yanzu shi ne, “Wadda Allah ya Yarda da Ita.”
Ƙasarki kuwa za a ce da ita, “Ta yi Aure da Farin Ciki,”
Domin Ubangiji ya ji daɗinki,
Zai kuwa zama kamar miji ga ƙasarki.