Ish 62:6-7
Ish 62:6-7 HAU
Ya Urushalima, na sa matsara a garukanki Ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Za su tuna wa Ubangiji da alkawaransa, Ba kuwa za su bari ya manta ba! Ba za su bari ya huta ba, sai ya ceci Urushalima tukuna, Ya sa ta zama birnin da dukan duniya za ta yaba wa.





