1
Ish 11:2-3
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ikon Ubangiji zai ba shi hikima, Da sani, da gwaninta yadda zai mallaki mutanensa. Zai kuwa san nufin Ubangiji, ya kuma yi tsoronsa, Zai ji daɗin yin hidimarsa. Ba zai yi shari'ar ganin ido ko ta waiwai ba.
Compare
Explore Ish 11:2-3
2
Ish 11:1
Gidan sarautar Dawuda kamar itacen da aka sare ne, amma kamar yadda rassa sukan toho daga cikin kututture, haka nan za a sami sabon sarki daga zuriyar Dawuda.
Explore Ish 11:1
3
Ish 11:4
Zai yi wa matalauta shari'a daidai. Zai kuma kāre hakkin masu tawali'u. Bisa ga umarninsa za a hukunta ƙasar, Mugaye za su mutu.
Explore Ish 11:4
4
Ish 11:5
Zai yi mulkin mutanensa da adalci da mutunci.
Explore Ish 11:5
5
Ish 11:9
A kan Sihiyona, dutse tsattsarka, Ba wani macuci ko mugu. Ƙasar za ta cika da sanin Ubangiji Kamar yadda tekuna suke cike da ruwa.
Explore Ish 11:9
6
Ish 11:6
Kyarketai da tumaki za su zauna tare lafiya. Damisoshi za su kwanta tare da 'yan awaki. 'Yan maruƙa da kwiyakwiyan zaki za su yi kiwo tare, Ƙananan yara ne za su lura da su.
Explore Ish 11:6
7
Ish 11:10
Rana tana zuwa sa'ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al'umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi.
Explore Ish 11:10
Home
Bible
Plans
Videos