1
Ibr 4:12
Littafi Mai Tsarki
HAU
Domin Maganar Allah rayayyiya ce, mai ƙarfin aiki, ta fi kowane irin takobi kaifi, har tana ratsa rai da ruhu, da kuma gaɓoɓi, har ya zuwa cikin ɓargo, tana kuma iya rarrabe tunanin zuciya da manufarta.
Compare
Explore Ibr 4:12
2
Ibr 4:16
Saboda haka, sai mu kusaci kursiyin Allah na alheri da amincewa, domin a yi mana jinƙai, a kuma yi mana alherin da zai taimake mu a kan kari.
Explore Ibr 4:16
3
Ibr 4:15
Gama Babban Firist da muke da shi ba marar juyayin kasawarmu ba ne, a'a, shi ne wanda aka jarabce shi ta kowace hanya da aka jarabce mu, amma bai yi zunubi ba.
Explore Ibr 4:15
4
Ibr 4:13
Ba wata halittar da za ta iya ɓuyar masa, amma kowane abu a fili yake, a shanye sosai a gaban idon wannan da za mu ba da lissafi a gabansa.
Explore Ibr 4:13
5
Ibr 4:14
To, tun da yake muna da Babban Firist mai girma, wanda ya ratsa sammai, wato Yesu Ɗan Allah, sai mu tsaya a kan abin da muka bayyana yarda a gare shi.
Explore Ibr 4:14
6
Ibr 4:11
Saboda haka, sai mu yi himmar shiga inuwar nan, kada wani yă kāsa shiga, saboda irin wannan rashin biyayya.
Explore Ibr 4:11