Ga shelar, “In ji Sairus Sarkin Farisa, Ubangiji, Allah na samaniya ya ba ni sarautar dukan duniya, ya kuma umarce ni in gina masa Haikali a Urushalima, ta ƙasar Yahuza. Duk wanda yake na mutanensa da yake nan Ubangiji Allahnsa ya kasance tare da shi, bari ya haura zuwa can Urushalima ta ƙasar Yahuza don ya sāke gina Haikalin Ubangiji, Allah na Isra'ila, shi ne Allah wanda ake masa sujada a Urushalima.