1
2Sar 5:1
Littafi Mai Tsarki
HAU
Na'aman kuwa, shugaban sojojin Sarkin Suriya, shi babba ne mai farin jini ƙwarai a wurin ubangidansa, domin ta wurinsa ne Ubangiji ya ba Suriyawa nasara. Shi mutum ne ƙaƙƙarfan jarumi, amma kuma kuturu ne.
Compare
Explore 2Sar 5:1
2
2Sar 5:10
Sai Elisha ya aiki manzo ya faɗa wa Na'aman ya tafi, ya yi wanka a Kogin Urdun har sau bakwai, naman jikinsa zai warke, zai tsarkaka.
Explore 2Sar 5:10
3
2Sar 5:14
Sai ya tafi ya yi wanka har sau bakwai a Kogin Urdun bisa ga maganar annabin Allah, sai naman jikinsa ya warke ya zama kamar na ƙaramin yaro, ya tsarkaka.
Explore 2Sar 5:14
4
2Sar 5:11
Amma Na'aman ya husata, ya yi tafiyarsa, yana cewa, “Na yi tsammani zai fito ya zo wurina ne, ya tsaya, ya yi kira sunan Ubangiji Allahnsa ya kaɗa hannunsa a wurin kuturtar, ya warkar da ni.
Explore 2Sar 5:11
5
2Sar 5:13
Amma barorinsa suka je wurinsa, suka ce masa, “Ranka ya daɗe, da a ce annabin ya umarce ka ka yi wani babban abu ne, ashe, da ba ka yi ba, balle wannan, da ya ce ka tafi ka yi wanka, ka tsarkaka?”
Explore 2Sar 5:13
6
2Sar 5:3
Wata rana sai ta ce wa uwargijyarta, “Da a ce ubangijina yana tare da annabin nan wanda yake Samariya, da ya warkar da shi daga kuturtarsa!”
Explore 2Sar 5:3
Home
Bible
Plans
Videos