1
2Sar 6:17
Littafi Mai Tsarki
HAU
Sa'an nan Elisha ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubangiji, ka buɗe idanunsa ya gani.” Ubangiji kuwa ya buɗe idanun saurayin, sai ga dutsen cike da dawakai da karusan wuta kewaye da Elisha.
Compare
Explore 2Sar 6:17
2
2Sar 6:16
Elisha kuwa ya ce masa, “Kada ka ji tsoro gama waɗanda suke tare da mu, sun fi waɗanda suke tare da su yawa.”
Explore 2Sar 6:16
3
2Sar 6:15
Da baran annabi Elisha ya tashi da sassafe, ya fita waje, sai ga sojoji, da dawakai, da karusai sun kewaye gari. Sai baran ya ce, “Wayyo, maigidana! Me za mu yi?”
Explore 2Sar 6:15
4
2Sar 6:18
Da Suriyawa suka gangaro wurinsa, sai Elisha ya yi addu'a ga Ubangiji, ya ce, “Ina roƙonka, ka bugi mutanen nan da makanta.” Ubangiji kuwa ya buge su da makanta bisa ga addu'ar Elisha.
Explore 2Sar 6:18
5
2Sar 6:6
Sa'an nan Elisha ya ce, “Daidai ina ya fāɗa?” Da ya nuna masa wurin, sai ya karyi tsumagiya, ya jefa a wurin, ya sa ruwan gatarin ya taso bisa kan ruwan.
Explore 2Sar 6:6
6
2Sar 6:5
Amma sa'ad da ɗaya daga cikinsu yake saran wani gungume, sai ruwan gatarinsa ya kwaɓe ya fāɗa a ruwa. Sai ya yi ihu, ya ce, “Wayyo, maigida, me zan yi? Abin aro ne.”
Explore 2Sar 6:5
7
2Sar 6:7
Sa'an nan ya ce, “Ɗauko.” Sai mutumin ya miƙa hannu, ya ɗauka.
Explore 2Sar 6:7
Home
Bible
Plans
Videos