1
2Sar 4:2
Littafi Mai Tsarki
HAU
Sai Elisha ya ce mata, “Me zan yi miki? Ki faɗa mini abin da kike da shi a gida.” Ta ce, “Ni dai ba ni da kome a cikin gidan, sai dai kurtun mai.”
Compare
Explore 2Sar 4:2
2
2Sar 4:1
Matar wani daga cikin ƙungiyar annabawa da ya rasu, ta kai kuka wurin Elisha, ta ce, “Maigidana, baranka, wato mijina, ya rasu, ka kuwa sani shi mai tsoron Ubangiji ne, amma wanda yake binsa bashi ya zo zai kwashe 'ya'yana biyu su zama bayinsa.”
Explore 2Sar 4:1
3
2Sar 4:3
Sa'an nan ya ce mata, “Ki tafi ki yi aron tandaye da yawa daga maƙwabtanki waɗanda ba kome a ciki.
Explore 2Sar 4:3
4
2Sar 4:4
Sa'an nan ki shiga ɗaki, ke da 'ya'yanki, ku rufe ƙofa. Ki ɗura mai cikin tandayen nan duka, bi da bi.”
Explore 2Sar 4:4
5
2Sar 4:6
Da tandayen suka cika ta ce wa ɗanta, “Kawo mini wani tandu.” Ɗan kuwa ya ce mata, “Ai, ba saura.” Sai man ya janye.
Explore 2Sar 4:6
6
2Sar 4:7
Sai ta koma ta faɗa wa annabi Elisha, shi kuwa ya ce mata, “Ki je ki sayar da man, ki biya bashin, abin da ya ragu kuwa ki ci, ke da 'ya'yanki.”
Explore 2Sar 4:7
7
2Sar 4:5
Sai ta tashi daga wurinsa, ta tafi ta shiga ɗaki tare da 'ya'yanta, ta rufe ƙofar. 'Ya'yan suna kawo tandaye tana ɗurawa.
Explore 2Sar 4:5
8
2Sar 4:34
Sa'an nan ya kwanta a kan yaron, ya sa bakinsa a bakin yaron, ya sa idanunsa a idanun yaron, hannuwansa kuma a kan na yaron, ya miƙe jikinsa akan yaron, sai jikin yaron ya yi ɗumi.
Explore 2Sar 4:34
Home
Bible
Plans
Videos