1
1Tas 5:16-18
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ku riƙa yin farin ciki a kullum. Ku riƙa yin addu'a ba fāsawa. Ku godiya ga Allah a kowane hali, domin shi ne nufin Allah a game da ku ta wurin Almasihu Yesu.
Compare
Explore 1Tas 5:16-18
2
1Tas 5:23-24
Allah kansa, mai zartar da salama, yă tsarkake ku sarai, ya kuma kiyaye ruhunku da ranku da jikinku ƙalau, ku kasance marasa abin zargi a ranar komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu. Wanda yake kiranku ɗin nan mai alkawari ne, zai kuwa zartar.
Explore 1Tas 5:23-24
3
1Tas 5:15
Ku lura fa, kada kowa ya rama mugunta da mugunta. Sai dai kullum ku nace yi wa juna aiki nagari, da kuma dukkan mutane.
Explore 1Tas 5:15
4
1Tas 5:11
Saboda haka, sai ku ƙarfafa wa juna zuciya, kuna riƙa inganta juna, kamar dai yadda kuke yi.
Explore 1Tas 5:11
5
1Tas 5:14
Muna kuma yi muku gargaɗi, 'yan'uwa, ku tsawata wa malalata, ku ƙarfafa masu rarraunar zuciya, ku taimaki marasa tsayayyiyar zuciya, ku yi haƙuri da kowa da kowa.
Explore 1Tas 5:14
6
1Tas 5:9
Allah bai ƙaddara mu ga fushinsa ba, sai dai ga samun ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu
Explore 1Tas 5:9
7
1Tas 5:5
Domin duk mutanen haske kuke, na rana kuma. Mu ba na dare ko na duhu ba ne.
Explore 1Tas 5:5
Home
Bible
Plans
Videos