1Tas 5:23-24
1Tas 5:23-24 HAU
Allah kansa, mai zartar da salama, yă tsarkake ku sarai, ya kuma kiyaye ruhunku da ranku da jikinku ƙalau, ku kasance marasa abin zargi a ranar komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu. Wanda yake kiranku ɗin nan mai alkawari ne, zai kuwa zartar.





