1
1Kor 3:16
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ashe, ba ku sani ku Haikalin Allah ne ba, Ruhun Allah kuma yana zaune a zuciyarku?
Compare
Explore 1Kor 3:16
2
1Kor 3:11
Harsashin kam, ba wanda yake iya sa wani dabam da wanda aka riga aka sa, wato, Yesu Almasihu.
Explore 1Kor 3:11
3
1Kor 3:7
Don haka da mai shukar, da mai banruwan, ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai, shi da ya girmar.
Explore 1Kor 3:7
4
1Kor 3:9
gama mu abokan aiki ne na Allah, ku kuwa gona ce ta Allah, ginin Allah kuma.
Explore 1Kor 3:9
5
1Kor 3:13
ai, aikin kowane mutum zai bayyana, domin ranar nan za ta tona shi, gama za a bayyana ta da wuta, wutar kuwa za ta gwada aikin kowa a san irinsa.
Explore 1Kor 3:13
6
1Kor 3:8
Da mai shukar, da mai banruwan, duk daidai suke, sai dai ko wanne zai sami tasa ladar gwargwadon wahalarsa
Explore 1Kor 3:8
7
1Kor 3:18
Kada kowa yă ruɗi kansa. In waninku ya zaci shi mai hikima ne, yadda duniya ta ɗauki hikima, sai yă mai da kansa marar hikima, domin ya sami zama mai hikima.
Explore 1Kor 3:18