1
1Kor 2:9
Littafi Mai Tsarki
HAU
Amma kuwa yadda yake a rubuce ke nan cewa, “Abubuwan da ido bai taɓa gani ba, Kunne bai taɓa ji ba, Zuciyar mutum kuma ba ta ko riya ba, Waɗanda Allah ya tanadar wa masu ƙaunarsa,”
Compare
Explore 1Kor 2:9
2
1Kor 2:14
Mutumin da ba shi da Ruhu yakan ƙi yin na'am da al'amuran Ruhun Allah, don wauta ne a gare shi, ba kuwa zai iya fahimtarsu ba, domin ta wurin ruhu ne ake rarrabewa da su.
Explore 1Kor 2:14
3
1Kor 2:10
mu ne Allah ya bayyana wa, ta wurin Ruhu, domin Ruhu shi yake fayyace kome, har ma zurfafan al'amuran Allah.
Explore 1Kor 2:10
4
1Kor 2:12
Mu kuwa ba ruhun duniya muka samu ba, sai dai Ruhu wanda yake daga wurin Allah, domin mu fahimci abubuwan da Allah ya yi mana baiwa hannu sake.
Explore 1Kor 2:12
5
1Kor 2:4-5
Jawabina da wa'azina, ba su danganta ga maganar rarrashi ko ta wayo ba, sai dai ga rinjaye na ikon Ruhu, kada bangaskiyarku ta dogara ga hikimar mutane, sai ga ƙarfin Allah.
Explore 1Kor 2:4-5