1
Mattiyu 27:46
Sabon Rai Don Kowa 2020
SRK
Wajen sa’a ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).
Compare
Explore Mattiyu 27:46
2
Mattiyu 27:51-52
A daidai wannan lokaci, sai labulen haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta jijjiga, duwatsu kuma suka farfashe. Kaburbura suka bubbuɗe, jikunan tsarkaka da yawa kuwa cikin waɗanda da suka mutu, suka tashi.
Explore Mattiyu 27:51-52
3
Mattiyu 27:50
Da Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sai ya saki ruhunsa.
Explore Mattiyu 27:50
4
Mattiyu 27:54
Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizar ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, “Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!”
Explore Mattiyu 27:54
5
Mattiyu 27:45
Daga sa’a ta shida, har zuwa sa’a ta tara, duhu ya rufe ƙasa duka.
Explore Mattiyu 27:45
6
Mattiyu 27:22-23
Bilatus ya yi tambaya, “To, me zan yi da Yesu wanda ake kira Kiristi?” Duka suka ce, “A gicciye shi!” Bilatus ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara tā da ihu, suna cewa, “A gicciye shi!”
Explore Mattiyu 27:22-23
Home
Bible
Plans
Videos