Da manyan firistoci da dattawa suka taru, sai suka ƙulla wata dabara, suka ba wa sojojin kuɗi mai yawa. Suka ce musu, “Ku, za ku ce, ‘Almajiransa ne sun zo da dare suka sace shi, lokacin da muke barci.’ In wannan labari ya kai kunnen gwamna, za mu lallashe shi, mu kuma kāre ku daga duk wata wahala.” Sai sojojin suka karɓi kuɗin, suka kuma yi kamar yadda aka umarce su. Wannan labarin kuwa shi ne ake bazawa ko’ina a cikin Yahudawa, har yă zuwa yau.