Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum. Gama a kwanaki kafin ruwan tsufana, mutane sun yi ta ci, sun kuma yi ta sha, suna aure, suna kuma aurarwa, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi; ba su kuwa san abin da yake faruwa ba sai da ruwan tsufana ya zo ya share su tas. Haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum.