Biểu trưng YouVersion
Biểu tượng Tìm kiếm

L.Fir 8

8
Keɓewar Haruna da 'Ya'yansa Maza
(Fit 29.1-37)
1Ubangiji ya ce wa Musa, 2“Ɗauki Haruna da 'ya'yansa maza, da rigunan, da man keɓewa, da bijimi na yin hadaya don zunubi, da raguna biyu, da kwandon abinci marar yisti. 3Ka kuma tattara jama'a duka a ƙofar alfarwa ta sujada.”
4Musa kuwa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi. Jama'ar kuwa suka tattaru a ƙofar alfarwa ta sujada. 5Musa ya faɗa wa taron jama'ar cewa “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta a yi.”
6Sai Musa ya fito da Haruna da 'ya'yansa maza, ya yi musu wanka. 7Ya sa wa Haruna zilaika, ya ɗaura masa ɗamara, ya sa masa taguwa, ya kuma sa masa falmaran, ya ɗaura masa ɗamarar falmaran wadda aka yi mata saƙar gwaninta. 8Ya maƙala masa ƙyallen maƙalawa a ƙirji, sa'an nan ya sa Urim da Tummin, a kan ƙyallen. 9Sai ya naɗa masa rawani, daga gaban rawanin ya sa allon zinariya, wato, kambi tsattsarka, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
10Sai Musa ya ɗauki man keɓewa ya shafa wa alfarwa ta sujada da dukan abin da yake cikinta, da haka ya tsarkake su. 11Ya yayyafa wa bagaden mai sau bakwai, ya kuma shafa wa bagaden da dukan kayayyakinsa, da daron da gammonsa, don ya tsarkake su. 12Ya zuba man keɓewa a kan Haruna, ya keɓe shi. 13Sai Musa kuma ya kawo 'ya'yan Haruna, maza, ya sa musu zilaiku, ya ɗaura musu ɗamaru, ya sa musu huluna kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
14Sa'an nan ya kawo bijimi na yin hadaya don zunubi, Haruna da 'ya'yansa maza, suka ɗibiya hannuwansu a kan kan bijimin. 15Sai Musa ya yanka shi, ya ɗibi jinin a yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden a kewaye, ya tsarkake bagaden, ya zuba jinin a gindin bagaden, ya keɓe shi don ya yi kafara dominsa. 16Sai ya ɗauki dukan kitsen da yake bisa kayan ciki da matsarmama, da ƙodoji biyu da kitsensu, ya ƙone su bisa bagaden. 17Amma ya ƙone naman bijimin da fatarsa da tarosonsa a bayan zangon kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
18Sa'an nan ya kawo rago na yin hadaya ta ƙonawa. Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan kan ragon. 19Sai ya yanka ragon, ya yayyafa jinin a bisa bagaden da kewayensa. 20Da aka yanyanka ragon gunduwa gunduwa, sai Musa ya ƙone kan, da gunduwoyin, da kitsen. 21Sa'ad da kuma aka wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sai ya ƙone ragon duka a bisa bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
22Musa ya kawo ɗayan ragon keɓewa, sai Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan kan ragon. 23Musa kuwa ya yanka shi, ya ɗibi jinin, ya sa a leɓatun kunnen dama na Haruna, da bisa babban yatsansa na hannun dama, da babban yatsa na ƙafar dama. 24Sai aka kawo 'ya'yan Haruna, maza, Musa kuma ya sa jinin a leɓatun kunnensu na dama, da manyan yatsotsi na hannuwansu na dama, da manyan yatsotsin ƙafafu na dama. Sa'an nan ya yayyafa jinin kewaye da bagaden. 25Ya kuma ɗauki kitsen, da wutsiya mai kitse, da dukan kitsen da yake bisa kayan ciki, da matsarmama da ƙodoji biyu da kitsensu, da cinyar dama. 26Daga cikin kwandon abinci marar yistin da yake a gaban Ubangiji, ya ɗauki waina guda marar yisti, da waina guda da aka yi da mai, da ƙosai guda. Sai ya ɗibiya su a bisa kitsen da cinyar dama. 27Ya sa waɗannan abubuwa duka a tafin hannuwan Haruna da na 'ya'yansa maza, ya miƙa abubuwan nan domin hadayar kaɗawa ga Ubangiji. 28Sa'an nan ya karɓe su daga tafin hannuwansu, ya ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a bisa bagaden don hadayar keɓewa, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 29Ya kuma ɗauki ƙirjin, ya kaɗa shi don hadayar kaɗawa ga Ubangiji. Wannan shi ne rabon Musa daga cikin ragon keɓewar, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
30Sa'an nan Musa ya ɗiba daga cikin man keɓewa da jinin da yake bisa bagaden, ya yayyafa wa Haruna da rigunansa, da 'ya'yansa maza da rigunansu. Da haka ya tsarkake Haruna da rigunansa, da 'ya'yansa maza da rigunansu.
31Sai Musa ya ce wa Haruna da 'ya'yansa maza, “Ku dafa naman a ƙofar alfarwa ta sujada, ku ci shi a wurin, da abincin da yake a cikin kwandon hadayar keɓewa, kamar yadda Ubangiji ya umarta, cewa, Haruna da 'ya'yansa maza za su ci shi. 32Sauran abin da ya ragu daga naman da abincin, sai ku ƙone su. 33Ba za ku fita daga cikin alfarwa ta sujada ba har kwana bakwai, wato, sai kwanakin keɓewarku sun cika, gama keɓewarku za ta ɗauki kwana bakwai. 34Abin da aka yi a wannan rana haka Ubangiji ya umarta a yi domin kafararku. 35A ƙofar alfarwa ta sujada za ku zauna dare da rana har kwana bakwai, kuna kiyaye umarnin Ubangiji don kada ku mutu, gama haka Ubangiji ya umarta.” 36Sai Haruna da 'ya'yansa maza suka yi dukan abin da Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.

Đang chọn:

L.Fir 8: HAU

Tô màu

Sao chép

So sánh

Chia sẻ

None

Bạn muốn lưu những tô màu trên tất cả các thiết bị của mình? Đăng ký hoặc đăng nhập