Fit 4
4
1Musa kuwa ya amsa ya ce, “Ai, ba za su gaskata ni ba, ba kuma za su kasa kunne ga maganata ba, gama za su ce, ‘Ubangiji bai bayyana gare ka ba.’ ”
2Amma Ubangiji ya ce masa, “Mene ne wannan a hannunka?”
Ya ce, “Sanda ne.”
3Ubangiji ya ce, “Jefa shi ƙasa.” Sai ya jefa shi ƙasa, sandan ya zama maciji, Musa kuwa ya yi gudunsa. 4Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka ka kama wutsiyarsa.” Ya miƙa hannunsa ya kama shi, ya zama sanda kuma a hannunsa. 5Sai Ubangiji ya ce, “Ta haka za su gaskata Ubangiji Allah na kakanninsu ne, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, ya bayyana gare ka.”
6Sai Ubangiji ya sāke ce masa, “Sa hannunka cikin ƙirjinka.” Sa'ad da ya fitar da shi, ga hannunsa a kuturce fari fat. 7Allah kuma ya ce masa, “Mai da hannunka cikin ƙirjinka.” Sai ya mai da hannunsa cikin ƙirjinsa. Sa'ad da ya fitar da shi, ga hannun ya koma kamar sauran jikinsa. 8Ubangiji kuma ya ce, “Idan kuma ba su gaskata ka ba, ba su kuma kula da mu'ujiza ta fari ba, ya yiwu su gaskata ta biyun. 9Idan ba su gaskata mu'ujizan nan biyu ba, ba su kuma kula da maganarka ba, sai ka ɗibi ruwa daga Kogin Nilu, ka zuba bisa busasshiyar ƙasa. Ruwan zai zama jini a bisa busasshiyar ƙasa.”
10Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangijina, ni ba mai lafazi ba ne, ban taɓa zama ba, ko a yanzu ma, bayan da ka yi magana da bawanka, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.”
11Ubangiji kuwa ya ce masa, “Wa ya yi bakin ɗan adam? Wa ya yi bebe ko kurma, ko mai gani ko makaho? Ko ba ni Ubangiji ba ne? 12Yanzu fa, tafi, zan kasance tare da bakinka, in koya maka abin da za ka faɗa.”
13Amma Musa ya ce, “Ya Ubangijina, in ka yarda, ka aiki wani.”
14Ubangiji kuwa ya hasala da Musa, ya ce, “Haruna ɗan'uwanka Balawe ba ya nan ne? Lalle na san shi ya iya magana, ga shi nan ma, yana fitowa ya tarye ka. Sa'ad da ya gan ka kuwa zai yi murna cikin zuciyarsa. 15Sai ka yi magana da shi. Ka kuma sa masa maganata a baka, zan kuwa kasance tare da bakinka da bakinsa. Zan kuma sanar da ku abin da za ku yi. 16Shi zai yi maka magana da jama'a, zai zama bakinka, kai kuwa za ka zama kamar Allah a gare shi. 17Za ka riƙe wannan sanda a hannunka, da shi za ka aikata mu'ujizan.”
Musa Ya Koma Masar
18Musa ya koma wurin Yetro, surukinsa, ya ce masa, “Ina roƙonka, ka bar ni in koma wurin 'yan'uwana a Masar, in ga ko a raye suke har yanzu.”
Sai Yetro ya ce wa Musa, “Ka tafi lafiya.”
19Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa a Madayana, ya koma Masar, gama dukan waɗanda suke neman ransa sun rasu. 20Saboda haka Musa ya ɗauki matarsa da 'ya'yansa maza, ya haushe su bisa kan jaki, ya koma ƙasar Masar, yana riƙe da sandan Allah a hannunsa. 21Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Sa'ad da ka koma Masar, sai ka kula, ka aikata a gaban Fir'auna dukan mu'ujizan da na sa cikin ikonka. Amma zan taurara zuciyarsa, don kada ya bar jama'a su fita. 22Za ka ce wa Fir'auna, Ubangiji ya ce, ‘Isra'ila ɗan fārina ne. 23#Fit 12.29 Na ce maka ka bar ɗana ya tafi domin ya bauta mini, amma in ka ƙi ka bar shi ya tafi, yanzu zan kashe ɗan fārinka.’ ”
24Ya zama kuwa sa'ad da Musa yake masauki a kan hanya sai Ubangiji ya gamu da shi, ya nema ya kashe shi. 25Sai Ziffora ta ɗauki ƙanƙara ta yanke loɓar ɗanta, ta taɓa gaban Musa da shi, ta ce, “Kai angon jini kake a gare ni.” 26Sa'an nan Ubangiji ya ƙyale shi. Ta kuma ce, “Kai angon jini ne,” saboda kaciyar.
27Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Tafi, ka taryi Musa cikin jeji.” Ya kuwa tafi ya tarar da shi a dutsen Allah, ya sumbace shi. 28Sa'an nan Musa ya faɗa wa Haruna abubuwan da Ubangiji ya aike shi ya yi, da dukan mu'ujizan da ya umarce shi ya aikata. 29Sai Musa da Haruna suka tafi suka tattara dukan dattawan Isra'ila. 30Haruna dai ya hurta wa dattawan al'amuran da Ubangiji ya faɗa wa Musa. Ya kuma aikata mu'ujizan a idanunsu. 31Dattawan kuwa suka gaskata. Sa'ad da suka ji Ubangiji ya ziyarci Isra'ilawa, ya kuma ga wahalarsu, sai suka sunkuya, suka yi masa sujada.
Đang chọn:
Fit 4: HAU
Tô màu
Sao chép
So sánh
Chia sẻ
Bạn muốn lưu những tô màu trên tất cả các thiết bị của mình? Đăng ký hoặc đăng nhập
@Bible Society of Nigeria 1979

: