Fit 35
35
Ka'idodin Ranar Hutawa
1Sai Musa ya tattara dukan taron jama'ar Isra'ila, ya ce musu, “Waɗannan su ne abubuwan da Ubangiji ya umarce ku ku yi. 2#Fit 20.8-11; 23.12; 31.15; 34.21; L.Fir 23.3; M.Sh 5.12-14 Cikin kwana shida za a yi aiki, amma rana ta bakwai Asabar ce tsattsarka ta Ubangiji ta hutawa sosai. Duk wanda ya yi kowane irin aiki a cikinta, sai a kashe shi. 3Ba za ku hura wuta a ranar Asabar a wuraren zamanku ba.”
Sadaka domin Yin Alfarwa ta Sujada
(Fit 25.1-9)
4Musa kuma ya ce wa taron jama'ar Isra'ila duka, “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta, 5ku karɓi sadaka daga cikinku saboda Ubangiji. Duk wanda ya yi niyya, bari ya kawo wa Ubangiji sadaka ta zinariya, da azurfa, da tagulla, 6da zane na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin, da gashin awaki, 7da fatun raguna da aka rina suka zama ja, da fatun awaki, da itacen ƙirya, 8da man fitila, da kayan yaji domin man keɓewa da turaren ƙonawa, 9da duwatsu masu tamani, da duwatsun da za a mammanne a falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.”
Kayayyakin Alfarwa ta Sujada
(Fit 39.32-43)
10“Bari dukan wanda yake da fasaha a cikinku ya zo, ya yi aikin da Ubangiji ya umarta a yi, 11wato aikin alfarwa ta sujada, da alfarwarta da murfinta, da maratayai, da katakanta da sandunanta, da dirkokinta, da kwasfanta, 12da akwati da sandunansa, da murfinsa, da labulen ƙofar. 13Da tebur da sandunansa, da kayayyakinsa duka, da gurasar ajiyewa, 14da alkuki don haske, da kayayyakinsa, da fitilunsa, da man fitila, 15da bagaden turaren ƙonawa da sandunansa, da man keɓewa mai ƙanshi, da turaren ƙonawa, da labulen ƙofar alfarwa ta sujada, 16da bagaden ƙona hadaya da ragarsa ta tagulla da sandunansa, da kayayyakinsa duka, da daro da gammonsa, 17da labulen farfajiya da dirkokinsa da kwasfansu, da labulen ƙofar farfajiyar, 18da turakun alfarwa, da turakun farfajiyar, da igiyoyinsu, 19da saƙaƙƙun tufafi na yin aiki a Wuri Mai Tsarki, da tsarkakakkun tufafin Haruna firist, da tufafin 'ya'yansa maza na aikin firist.”
Jama'a sun Kawo Sadaka
20Sa'an nan dukan taron jama'ar Isra'ila suka tashi daga wurin Musa. 21Duk wanda ya yi niyya, da wanda ruhunsa ya iza shi ya kawo wa Ubangiji sadaka don yin alfarwa ta sujada, da dukan ayyukansa, da tsarkakakkun tufafi. 22Sai dukan mata da maza waɗanda suke da niyya, suka kawo kayayyakin ƙawanya, wato da 'yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri iri. Kowane mutum ya ba da sadaka ta zinariya ga Ubangiji. 23Kowane mutum da aka iske shi yana da shuɗi, ko shunayya, ko mulufi, ko lallausan lilin, ko gashin awaki, ko fatun raguna da aka rina suka zama ja, ko fatun awaki, ya kawo su. 24Kowane ne wanda ya iya, ya ba da sadaka ta azurfa, da ta tagulla ga Ubangiji. Duka kuma wanda aka iske shi yana da itacen ƙirya wanda zai yi amfani a cikin aikin, ya kawo shi. 25Dukan mata masu hikima suka kaɗa zare da hannuwansu, suka kawo zaren da suka kaɗa na shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin. 26Sai kuma dukan mata masu hikima, waɗanda zuciyarsu ta iza su, suka kaɗa zare da gashin awaki. 27Su shugabanni suka kawo duwatsu masu daraja da za a jera a kan falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. 28Suka kuma kawo kayan yaji, da man fitila, da man keɓewa, da turaren ƙonawa. 29Sai dukan mata da maza na Isra'ilawa waɗanda zuciyarsu ta iza su, suka kawo kowane irin abu domin yin aikin da Ubangiji ya umarci Musa. Suka kawo sadaka ta yardar rai ga Ubangiji.
Waɗanda Suka Yi Aikin Alfarwa ta Sujada
(Fit 31.1-11)
30Sai Musa ya ce wa Isra'ilawa, “Ga shi, Ubangiji ya zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza. 31Ya cika shi da ruhu na hikima, da basira, da sani, da fasaha na iya yin kowane irin aiki. 32Domin ƙirƙiro zāne-zāne na gwaninta, waɗanda za a yi da zinariya, da azurfa, da tagulla. 33Haka kuma wajen sassaƙar duwatsu na jerawa, da sassaƙar itace, da kowane irin aiki na gwaninta. 34Ubangiji ya ba Bezalel, da Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, hikimar koya wa waɗansu sana'a. 35Gama ya cika su da hikima ta yin kowane irin aiki na sassaƙa da na zāne-zāne, da na yin ɗinke-ɗinke da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin, da na yin saƙa. Sun iya yin kowane irin aiki da yin zāne-zāne.
Đang chọn:
Fit 35: HAU
Tô màu
Sao chép
So sánh
Chia sẻ
Bạn muốn lưu những tô màu trên tất cả các thiết bị của mình? Đăng ký hoặc đăng nhập
@Bible Society of Nigeria 1979

: