Fit 30
30
Bagaden Ƙona Turare
(Fit 37.25-28)
1“Za ku yi bagaden ƙona turare. Za ku yi shi da itacen ƙirya. 2Tsawonsa da fāɗinsa kamu guda guda ne, zai zama murabba'i, amma tsayinsa ya zama kamu biyu. Za a haɗa zankayensa su zama ɗaya da shi. 3Za ku dalaye shi, da bisansa, da gyaffansa, da zankayensa da zinariya tsantsa. Ku kuma yi masa dajiyar zinariya. 4Za ku yi masa ƙawanya biyu na zinariya a ƙarƙashin dajiyar gefe da gefe, daura da juna. Ƙawanen za su zama inda za a zura sandunan ɗaukarsa. 5Za ku yi sandunan da itacen ƙirya, ku dalaye su da zinariya. 6Sai ku ajiye bagaden a gaban labulen akwatin alkawari da murfin akwati inda zan sadu da kai. 7Haruna kuwa zai ƙona turare mai ƙanshi a bisansa kowace safiya lokacin da yake gyarta fitilun. 8Zai kuma ƙona turaren sa'ad da ya kunna fitilun da almuru. Za a riƙa ƙona turare kullum a gaban Ubangiji dukan zamananku. 9Ba za a ƙona wani irin turare dabam ba a bisansa, ba kuma za a miƙa hadaya ta ƙonawa, ko ta gari, ko ta sha, a bisansa ba. 10Sau ɗaya a shekara Haruna zai yi kafara a bisa zankayensa. Zai yi kafara a bisansa da jinin hadaya don zunubi ta yin kafara. Za a riƙa yin wannan dukan zamananku, gama bagaden mai tsarki ne ga Ubangiji.”
Kuɗin Haikali
11Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, 12“A sa'ad da za ku ƙidaya Isra'ilawa, sai ko wannensu ya biya fansar kansa ga Ubangiji domin kada annoba ta buge su lokacin da za ku ƙidaya su. 13#Fit 38.25,26; Mat 17.24 Dukan wanda aka lasafta shi cikin ƙidayar kuwa zai biya kuɗi bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. Tilas kowanne ya biya wannan, gama sadaka ce ga Ubangiji. 14Duk wanda aka lasafta shi cikin ƙidayar tun daga mai shekara ashirin ko fi, zai ba da wannan sadaka ga Ubangiji. 15Lokacin da kuke ba da wannan sadaka ga Ubangiji saboda kafarar rayukanku, mai samu ba zai zarce ba, matalauci kuma ba zai ba da abin da ya gaza abin da aka ƙayyade ba. 16Za ku karɓi kuɗin nan na kafara daga wurin Isra'ilawa, ku ajiye shi domin aiki a alfarwa ta sujada. Zai zama abin tunawa ga Isra'ilawa a gaban Ubangiji, don su yi kafarar kansu.”
Daron Tagulla na Wanke Hannu
17Ubangiji ya kuma ce wa Musa, 18#Fit 38.8 “Sai ku yi daro da tagulla don wanka. Ku yi masa gammo da tagulla, ku ajiye shi tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, ku zuba ruwa a ciki. 19A wurin ne Haruna da 'ya'yansa maza za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu. 20Sa'ad da suke shiga cikin alfarwa ta sujada ko sa'ad da suke kusatar bagade don su miƙa hadaya ta ƙonawa da wuta ga Ubangiji, sai su yi wanka don kada a kashe su. 21Su wanke hannuwansu da ƙafafunsu don kada su mutu. Yin wannan zai zama musu da zuriyarsu farilla dukan zamanansu.”
Man Keɓewa da Turare
22 #
Fit 37.29
Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 23“Ɗauki kayan yaji masu kyan gaske, ruwan mur na shekel ɗari biyar, da kirfa mai daɗin ƙanshi na shekel ɗari biyu da hamsin, da turaren wuta mai ƙanshi na shekel ɗari biyu da hamsin, 24da kashiya na shekel ɗari biyar bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi, da moɗa ɗaya na man zaitun. 25Da waɗannan za ku yi man keɓewa mai tsarki yadda mai yin turare yake yi, zai zama man keɓewa mai tsarki. 26Za a shafa wa alfarwa ta sujada da akwatin alkawari wannan mai. 27A kuma shafa wa teburin da kayayyakinsa, da alkukin da kayayyakinsa, da bagaden ƙona turare, 28da bagaden hadaya ta ƙonawa da kayayyakinsa, da daron da gammonsa. 29Ta haka za a tsarkake su domin su zama masu tsarki sosai. Duk abin da ya taɓa su zai tsarkaka. 30Za ka zuba wa Haruna da ya'yansa maza mai, ka keɓe su domin su zama firistocina masu yi mini aiki. 31Sai ka faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Wannan mai, mai tsarki ne a gare ni domin keɓewa a dukan zamananku. 32Ba za a shafa wa kowa ba, ba kuma za a yi wani mai irinsa ba, gama man tsattsarka ne, saboda haka zai kasance tsattsarka a gare ku. 33Duk wanda ya yi wani irinsa ko kuwa ya shafa wa wani, za a raba shi da jama'arsa’ ”
34Ubangiji ya ce wa Musa, “Ɗauki kayan yaji masu ƙanshi, su stakte, da onika, da galbanum tare da lubban. Su zama daidai wa daida. 35Da waɗannan za a yi turare yadda mai yin turare yake yi, a sa masa gishiri, ya zama tsabtatacce, tsarkakakke. 36A ɗauki kaɗan daga ciki, a niƙa, sa'an nan a ɗiba daga ciki, a ajiye a gaban akwatin alkawari a cikin alfarwa ta sujada a inda zan sadu da kai. Wannan turare zai zama muku mafi tsarki. 37Irin turaren nan da za ku yi, ba za ku yi wa kanku irinsa ba. Zai zama abu mai tsarki a gare ku, gama na Ubangiji ne. 38Duk wanda ya yi irin turaren nan don amfanin kansa, za a raba shi da jama'arsa.”
Đang chọn:
Fit 30: HAU
Tô màu
Sao chép
So sánh
Chia sẻ
Bạn muốn lưu những tô màu trên tất cả các thiết bị của mình? Đăng ký hoặc đăng nhập
@Bible Society of Nigeria 1979

: