Biểu trưng YouVersion
Biểu tượng Tìm kiếm

Fit 26

26
Alfarwa, Wato Wurin da Allah Zai Zauna
(Fit 36.8-38)
1“Alfarwar kanta, za ku yi ta da labule goma na lilin mai laushi ninki biyu, da ulu mai launi shuɗi, da launi shunayya da launi ja. Waɗannan labule za a yi musu zānen siffofin kerubobi, aikin gwani. 2Tsawon kowane labule zai zama kamu ashirin da takwas, fāɗinsa kuwa kamu huɗu. Labulen su zama daidai wa daida. 3Labule biyar biyar, za a harhaɗa, a ɗinka. 4Ku kuma yi wa labulen nan biyu hantuna na shuɗi a karbunsu na bisa. 5Za ku yi wa kowane labule hantuna hamsin. Hantunan labulen nan biyu su yi daura da juna. 6Za ku yi maɗauri guda hamsin da zinariya don a haɗa hantuna na labulen nan domin alfarwa ta zama ɗaya.
7“Ku yi labule goma sha ɗaya da gashin awaki, da za ku rufe alfarwar da shi. 8Tsawon kowanne zai zama kamu talatin, fāɗinsa kamu huɗu. Labulen za su zama daidai wa daida. 9Za ku harhaɗa biyar ku ɗinka. Haka kuma za ku yi da sauran shidan. Ku ninka na shida riɓi biyu, ku yi labulen ƙofar alfarwa da shi. 10Za ku kuma sa hantuna hamsin a karbun labulen daga bisa. Haka nan kuma za a sa hantuna hamsin a karbun ɗayan. 11Sa'an nan ku yi maɗauri hamsin da tagulla, ku ɗaura hantunan da su don ku haɗa alfarwar ta zama ɗaya. 12Ragowar rabin labulen da yake a bisa alfarwar, sai a bar shi yana reto a bayan alfarwar. 13Kamu ɗayan da ya ragu a kowane gefe na tsawon, sai a bar shi yana reto a kowane gefe domin ya rufe alfarwar. 14Za ku yi abin rufe alfarwa da fatun raguna da aka rina ja, za ku kuma yi wani abin rufewa da fatun da aka jeme.
15“Za ku yi alfarwar da katakon itacen ƙirya. Za ku kakkafa su a tsaye. 16Tsawon kowane katako zai zama kamu goma, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi. 17Za a fiƙe kan kowane katako. Haka za ku yi da dukan katakan. 18Za ku shirya katakan alfarwa kamar haka, katakai ashirin wajen gefen kudu. 19Ku kuma yi kwasfa arba'in da azurfa da za a sa wa katakan nan ashirin. Za a sa kawunan katakan da aka fiƙe a cikin kwasfa. 20Za ku kuma kafa katakai ashirin wajen gefen arewa na alfarwar. 21Haka kuma za ku yi kwasfa arba'in da azurfa dominsu. Kwasfa biyu domin kowane katako. 22A wajen yamma ga alfarwa kuma ku kafa katakai shida. 23Ku kuma sa katakai biyu a kowace kusurwa ta yamma a alfarwa. 24Katakan nan kuwa, sai a haɗa su daga ƙasa zuwa sama, a ɗaure. Haka za a yi da katakan kusurwan nan biyu. Za su zama na kusurwa biyu. 25Za a sami katakai takwas da kwasfansu na azurfa guda goma sha shida, kowane katako yana da kwasfa biyu.
26“Sai ku yi sanduna da itacen ƙirya. Sanduna biyar domin katakai na gefe ɗaya. 27Biyar kuma domin katakai na wancan gefe. Har yanzu kuma biyar domin katakai na gefen yamma. 28Sandan da yake tsakiyar katakan zai bi daga wannan gefe zuwa ƙarshen wancan gefe. 29Za ku dalaye katakan da zinariya, ku kuma yi musu ƙawanen zinariya inda za a sa sandunan. Za ku dalaye sanduna kuma da zinariya. 30Ta haka za ku yi alfarwar bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.
31“Za ku yi labule da lallausan zaren lilin, mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A yi shi da gwaninta, a zana siffofin kerubobi a kansa. 32Ku rataye shi a bisa dirkoki huɗu nan itacen ƙirya waɗanda aka dalaye da zinariya, da maratayansu na zinariya waɗanda aka sa cikin kwasfa huɗu na azurfa. 33#Ibr 6.19; 9.3-5 Za ku sa labulen a ƙarƙashin maɗauran, sa'an nan ku shigar da akwatin alkawari a bayan labulen. Labulen zai raba tsakanin Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki. 34Ku sa murfin a bisa akwatin alkawari a Wuri Mafi Tsarki. 35Sai ku sa teburin a gaban labulen wajen arewa, ku kuma sa alkukin a kudancin alfarwar daura da teburin. 36Haka nan kuma za ku yi wa ƙofar alfarwa makari da lallausan zaren lilin mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi, aikin mai gwaninta. 37Ku yi dirkoki biyar da itacen ƙirya saboda makarin, ku dalaye su da zinariya. Ku kuma yi maratayansu da zinariya. Ku yi wa waɗannan dirkoki kwasfa biyar da tagulla.”

Đang chọn:

Fit 26: HAU

Tô màu

Sao chép

So sánh

Chia sẻ

None

Bạn muốn lưu những tô màu trên tất cả các thiết bị của mình? Đăng ký hoặc đăng nhập