to, hannuna zai auka wa dabbobinka cikin sauruka, da dawakai, da jakai, da raƙuma, da shanu, da tumaki, da awaki, da annoba mai tsanani. Zan raba tsakanin dabbobin Isra'ilawa, da na Masarawa. Ko ɗaya daga cikin dabbobin Isra'ilawa ba zai mutu ba. Na riga na sa lokacin.