YouVersion Logo
Search Icon

Amos 1

1
Horon Allah a kan Maƙwabtan Isra'ila
1 # 2Sar 15.1-7; 2Tar 26.1-23; 2Sar 14.23-29 Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa. Allah ya bayyana wa Amos wannan saƙo, tun shekara biyu kafin girgizar duniya, a lokacin da Azariya yake sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa yake sarautar Isra'ila.
2 # Yow 3.16 Amos ya ce,
“Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona,
Muryarsa za ta yi tsawa daga
Urushalima.
Da jin wannan, sai wuraren kiwo za
su bushe,
Ƙwanƙolin Dutsen Karmel, da yake
kore zai yi yaushi.”
Suriya
3 # Ish 17.1-3; Irm 49.23-27; Zak 9.1 Ubangiji ya ce,
“Mutanen Dimashƙu sun ci gaba da
yin zunubi.
Hakika, zan hukunta su,
Don sun zalunci mutanen Gileyad da
zalunci mai tsanani.
4Don haka zan aukar da wuta a kan
fādar Sarkin Suriya.
Za ta ƙone kagarar Ben-hadad,
sarki.
5Zan ragargaje ƙyamaren ƙofofin
birnin Dimashƙu,
In kawar da masu sarautar Bet-eden
da na kwarin Awen.
Za a kwashe mutanen Suriya ganima
zuwa ƙasar Kir.”
Filistiya
6 # Ish 14.29-31; Irm 47.1-7; Eze 25.15-17; Yow 3.4-8; Zaf 2.4-7; Zak 9.5-7 Ubangiji ya ce,
“Mutanen Gaza sun ci gaba da yin
zunubi.
Hakika, zan hukunta su,
Don sun kwashe al'umma duka, sun
sayar wa mutanen Edom.
7Saboda haka zan aukar da wuta a
kan garun Gaza ta ƙone kagarar
birnin.
8Zan kawar da masu sarautar biranen
Ashdod da Ashkelon,
Zan karɓe sandan mulkin Ekron.
Sauran Filistiyawa da suka ragu
kuma,
Za su mutu duka.”
Taya
9 # Ish 23.1-18; Eze 26.1—28.19; Yow 3.4-8; Zak 9.1-4; Mat 11.21,22; Luk 10.13,14 Ubangiji ya ce,
“Mutanen Taya sun ci gaba da yin
zunubi.
Hakika, zan hukunta su,
Don sun kwashe mutanen sun kai
ƙasar Edom.
Suka karya yarjejeniyar abuta wadda
suka yi.
10Saboda haka zan aukar da wuta a
kan garun Taya,
Ta ƙone kagarar birnin.”
Edom
11 # Ish 34.5-17; 63.1-6; Irm 49.7-22; Eze 25.12-14; 35.1-15; Oba 1.1-14; Mal 1.2-5 Ubangiji ya ce,
“Mutanen Edom sun ci gaba da yin
zunubi.
Hakika, zan hukunta su,
Don sun farauci 'yan'uwansu,
Isra'ilawa,
Suka ƙi su nuna musu jinƙai.
Ba su yarda su huce daga fushinsu
ba.
12Saboda haka zan aukar da wuta a
kan Teman,
Ta ƙone kagarar Bozara.”
Ammon
13 # Irm 49.1-6; Eze 21.28-32; 25.1-7; Zaf 2.8-11 Ubangiji ya ce,
“Mutanen Ammon sun ci gaba da yin
zunubi.
Hakika, zan hukunta su,
Don haɗamarsu ta ƙasa,
Suka tsaga mata masu ciki a
Gileyad.
14Saboda haka zan aukar da wuta a
kan garun Rabba,
Ta ƙone kagarar birnin.
Za a yi kururuwa a ranar yaƙi,
Faɗan kuwa zai yi rugugi kamar
hadiri.
15Sarkinsu da manyan mutanensu za a
kai su wata ƙasa dabam.”

Currently Selected:

Amos 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy