Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa. Allah ya bayyana wa Amos wannan saƙo, tun shekara biyu kafin girgizar duniya, a lokacin da Azariya yake sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa yake sarautar Isra'ila.
Amos ya ce,
“Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona,
Muryarsa za ta yi tsawa daga
Urushalima.
Da jin wannan, sai wuraren kiwo za
su bushe,
Ƙwanƙolin Dutsen Karmel, da yake
kore zai yi yaushi.”