YouVersion Logo
Search Icon

Zak 2

2
Wahayin Mutum da Igiyar Awo da Zakariya Ya Gani
1Da na ɗaga idona, sai ga wani mutum yana riƙe da igiyar awo. 2Sai na ce, “Ina za ka?”
Ya ce mini, “Zan tafi in auna Urushalima don in san fāɗinta da tsawonta.”
3Sai ga mala'ikan da yake magana da ni, ya fita, sai wani mala'ika kuma ya zo ya sadu da shi. 4Ya ce masa, “Ka yi gudu, ka faɗa wa saurayin can, cewa za a zauna a Urushalima kamar a ƙauyuka marasa garu, saboda yawan mutane da dabbobi da suke cikinta. 5Gama zan zama mata garu na wuta kewaye da ita, zan zama daraja a tsakiyarta, in ji Ubangiji.”
An Kirawo 'Yan Bautar Talala
6Ubangiji ya ce, “Yanzu ku gudu daga ƙasar arewa, gama na warwatsa ku a waje kamar iska ta kusurwoyi huɗu na duniya! 7Ya ke Sihiyona, ku tsere, ku waɗanda kuke zaune a Babila.”
8Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Bayan ɗaukaka ya aike ni zuwa wurin al'umman duniyan nan da suka washe ku, gama wanda ya taɓe ku, ya taɓi ƙwayar idona. 9Ga shi, zan nuna ikona a kansu, za su kuwa zama abin waso ga waɗanda suka bauta musu. Sa'an nan za ku sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni.
10“Ki raira waƙa, ki yi farin ciki, ya Sihiyona, gama ina zuwa, in zauna a tsakiyarki! Ni Ubangiji na faɗa.
11“A wannan rana al'umman duniya da yawa za su haɗa kai da Ubangiji, za su kuwa zama jama'ata, ni kuma zan zauna a tsakiyarki. Za ki sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni gare ki. 12Yahuza za ta zama abin mallakar Ubangiji a cikin tsattsarkar ƙasar. Zai kuma zaɓi Urushalima.”
13Bari dukan 'yan adam su yi tsit a gaban Ubangiji, gama ya taso daga wurin zamansa mai tsarki.

Currently Selected:

Zak 2: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy