YouVersion Logo
Search Icon

Rom 8

8
Rayuwa a Cikin Ruhu
1Saboda haka a yanzu, ba sauran kayarwa ga waɗanda suke na Almasihu Yesu. 2Ka'idar nan ta Ruhu mai ba da rai da yake ga Almasihu Yesu ta 'yanta ni daga ka'idar zunubi da ta mutuwa. 3Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi. 4Wannan kuwa domin a cika hakkokin Shari'a ne a gare mu, mu da ba zaman halin mutuntaka muke yi ba, sai dai na Ruhu. 5Masu zaman halin mutuntaka, ai, ƙwallafa ransu ga al'amuran halin mutuntaka suke yi, masu zaman Ruhu kuwa ga al'amuran Ruhu. 6Ƙwallafa rai ga al'amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga ala'muran Ruhu kuwa rai ne da salama. 7Don ƙwallafa rai ga al'amuran halin mutuntaka gāba ne da Allah, gama ba ya bin Shari'ar Allah, ba kuwa zai iya ba. 8Masu zaman halin mutuntaka, ba dama su faranta wa Allah rai.
9Amma ku kam, ba masu zaman halin mutuntaka ba ne, masu zaman Ruhu ne, in dai har Ruhun Allah yana zaune a zuciyarku. Duk wanda ba shi da Ruhun Almasihu kuwa, ba na Almasihu ba ne. 10In kuwa Almasihu yana a zuciyarku, ba ruwan jikinku da zunubi ke nan, Ruhu kuwa rai ne a gare ku saboda kun sami adalcin Allah. 11#1Kor 3.16 In kuwa Ruhun wannan da ya ta da Yesu daga matattu yana zaune a zuciyarku, to, shi da ya ta da Almasihu Yesu daga matattu zai kuma raya jikin nan naku mai mutuwa, ta wurin Ruhunsa da yake a zaune a zuciyarku.
12Domin haka, 'yan'uwa, kun ga halin mutuntaka ba shi da wani hakki a kanmu har da za mu yi zamansa. 13In kuna zaman halin mutuntaka, za ku mutu ke nan, amma in da ikon Ruhu kuka kashe ayyukan nan na halin mutuntaka, sai ku rayu. 14Duk waɗanda Ruhun Allah yake bishe su, su ne 'ya'yan Allah. 15#Gal 4.5-7#Mar 14.36; Gal 4.6 Ai, ruhun da kuka samu ba na bauta ba ne, har da za ku koma zaman tsoro. A'a, na zaman 'ya'ya ne, har muna kira, “Ya Abba! Uba!” 16Ruhu da Kansa ma, tare da namu ruhu suna yin shaida, cewa mu 'ya'yan Allah ne. 17In kuwa 'ya'ya muke, ashe, magāda ne kuma, magādan Allah, abokan gādo kuma da Almasihu, in dai har muna shan wuya tare da shi, a kuwa ɗaukaka mu tare da shi.
18Ai, a ganina, wuyar da muke sha a wannan zamani, ba ta isa a kwatanta ta da ɗaukakar da za a bayyana mana ba. 19Ga shi, duk halitta tana marmari, tana ɗokin ganin bayyanar 'ya'yan Allah. 20#Far 3.17-19 An sarayar da halitta ta zama banza, ba da nufinta ba, amma da nufin wanda ya sarayar da ita. Duk da haka, akwai sa zuciya, 21gama za a 'yantar da halitta da kanta ma, daga bautar ruɓewa, domin ta sami 'yancin nan, na ɗaukaka na 'ya'yan Allah. 22Mun dai san dukan halitta tana nishi, na shan azaba kuma irin ta mai naƙuda, har ya zuwa yanzu. 23#2Kor 5.2-4 Banda haka ma, har mu kanmu da muka riga muka sami Ruhu Mai Tsarki, wanda yake shi ne nunan fari, a cikin abubuwan da za mu samu, muna nishi a ranmu, muna ɗokin cikar zamanmu na 'ya'yan Allah, wato, fansar jikin nan namu ke nan. 24Sa'ad da aka cece mu ne muka yi wannan sa zuciya. Amma kuwa, ai, sa zuciya ga abin da aka samu, ba sa zuciya ba ce. Wa yake sa zuciya ga abin da ya samu? 25In kuwa muna sa zuciya ga abin da ba mu samu ba, da jimiri mukan yi sauraronsa.
26Haka kuma Ruhu yake yi mana taimako a kan gajiyawarmu, domin ba mu ma san abin da ya kamata mu roƙa ba, amma Ruhu da kansa yana yi mana roƙo da nishe-nishen da ba su hurtuwa. 27Amma shi mai fayyace zukatanmu ya san abin da Ruhu yake niyya, domin bisa ga nufin Allah ne Ruhu yake yi wa tsarkaka roƙo.
Mun Zarce A Ce da Mu Masu Nasara Ne
28Mun kuma sani al'amura duka suna aikatawa tare, zuwa alheri ga waɗanda suke ƙaunar Allah, wato, waɗanda suke kirayayyu bisa ga nufinsa. 29Waɗanda Allah ya riga ya zaɓa tun tuni, su ne ya ƙaddara su ɗauki kamannin Ɗansa, domin shi Ɗan yă zama na farko a cikin 'yan'uwa masu yawa. 30Waɗanda ya ƙaddarar nan kuwa, su ne ya kira. Waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar. Waɗanda ya kuɓutar ɗin kuwa, su ne ya ɗaukaka.
31To, me kuma za mu ce a game da haka? Da yake Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu? 32Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai ba mu kome tare da shi hannu sake ba? 33Wa zai ɗora wa zaɓaɓɓun Allah laifi? Allah ne yake kuɓutar da su! 34Wa zai hukunta su? Almasihu Yesu wanda ya mutu, ko kuwa a ce wanda ya tashi daga matattu, shi ne wanda yake zaune dama ga Allah, shi ne kuwa wanda yake roƙo saboda mu! 35Wa zai iya raba mu da ƙaunar da Almasihu yake yi mana? Ƙunci ne? ko masifa? ko tsanani? ko yunwa? ko huntanci? ko hatsari? ko takobi? 36#Zab 44.22 Kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Saboda kai ne ake kashe mu yini zubur,
An lasafta mu kamar tumakin yanka.”
37Duk da haka kuwa a cikin wannan hali duka, har mun zarce ma a ce mana masu nasara, ta wurin wannan da ya ƙaunace mu. 38Domin na tabbata, ko mutuwa ce, ko rai, ko mala'iku, ko manyan mala'iku, ko al'amuran yanzu, ko al'amura masu zuwa, ko masu iko, 39ko tsawo, ko zurfi, kai, ko kowace irin halitta ma, ba za su iya raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu ba.

Currently Selected:

Rom 8: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in