Rom 2
2
Hukuncin Allah Daidai Ne
1 #
Mat 7.1; Luk 6.37 Saboda haka ba ka da wata hujja, kai mutum, ko kai wane ne da kake ganin laifin wani. A yayin da kake ganin laifin wani, ai, kanka kake hukunta wa, don ga shi, kai mai ganin laifin wani, kai ma haka kake yi. 2Mun dai san hukuncin Allah a kan masu yin haka daidai ne. 3Ya kai mutum, kai da kake ganin laifin masu yin haka, alhali kuwa kai kanka, kana yinsu, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne? 4Ko kuwa kana raina yalwar alherinsa, da jimirinsa, da kuma haƙurinsa ne? Ashe, ba ka sani ba alherin Allah yana jawo ka zuwa ga tuba? 5Amma ga shi, saboda ƙeƙasasshiyar zuciyarka marar tuba, kana nema wa kanka fushin Allah a ranar fushi, sa'ad da za a bayyana hukuncin Allah macancani. 6#Zab 62.12; K.Mag 24.12 Allah ne zai saka wa kowa gwargwadon aikinsa. 7Waɗanda suke neman daraja da ɗaukaka da kuma dawwama ta wurin naciyarsu ga aikata nagarta, zai saka musu da rai madawwami. 8Waɗanda suke masu sonkai, da waɗanda suke ƙin bin gaskiya, da masu bin rashin adalci, zai saka musu da fushi da hasala. 9Duk waɗanda suke aikata mugunta za su sha wahala da masifa, da fari Yahudawa, sa'an nan kuma al'ummai. 10Amma Allah zai ba da daraja, da ɗaukaka, da salama ga dukan waɗanda suke aikata nagarta, da fari ga Yahudawa, sa'an nan ga al'ummai. 11#M.Sh 10.17 Domin kuwa, Allah ba ya nuna tara.
12Ɗaukacin waɗanda suka yi zunubi a rashin sanin Shari'a, za su hallaka ne ba tare da Shari'a ba. Ɗaukacin waɗanda suka yi zunubi a ƙarƙashin Shari'a kuwa, za a hukunta su ta hanyar Shari'a. 13Don ba ta jin shari'ar kawai mutum yake samun kuɓuta ga Allah ba, sai dai masu aikata ta, su ne za su kuɓuta. 14In al'ummai, su da ba su da Shari'a, jikinsu ya ba su suka bi umarnin Shari'a, ko da yake ba su da Shari'ar, ashe kuwa, suna da shari'a ke nan. 15Ayyukansu sun nuna, cewa abin da Shari'a ta umarta a rubuce yake a cikin zukatansu, lamirinsu kuwa yana shaidawa, tunaninsu kuwa yana zarginsu, ko kuma yana kāre su. 16A wannan rana Allah zai yi wa 'yan adam shari'a a kan asiransu, ta wurin Yesu Almasihu, bisa ga bishara da nake wa'azinta.
Yahudawa da Shari'a
17To, in ka ce kai Bayahude ne, cewa ka dogara da Shari'a, har kana taƙama da Allah, 18ka san abin da yake so, da yake kuma ka karantu da Shari'a, ka iya bambancewa da abubuwa mafifita, 19har ka amince kai kanka jagoran makafi ne, haske ga waɗanda suke a cikin duhu, 20mai horon marasa azanci, mai koya wa sababbin shiga, don a cikin Shari'ar kana da ainihin sani da ainihin gaskiya, 21to, kai mai koya wa wani, ba ka koya wa kanka? Kai mai wa'azin kada a yi sata, shin, kai ba ka yi ne? 22Kai mai cewa kada a yi zina, kai ba ka yi ne? Kai mai ƙyamar gumaka, ba ka sata a ɗakin gunki ne? 23Kai mai taƙama da Shari'a, ashe, ba wulakanta Allah kake yi ba ta keta Shari'ar? 24#Ish 52.5 Yadda yake a rubuce cewa, “A sanadinku ne al'ummai suke saɓon sunan Allah.”
25Lalle yin kaciya yana da amfani, in dai kana bin Shari'ar. Amma in kai mai keta shari'ar ne, kaciyarka ba a bakin kome take ba. 26In kuwa marar kaciya yana kiyaye farillan Shari'a, ashe, ba sai a lasafta rashin kaciyarsa a kan kaciya ba? 27Ashe, wanda rashin kaciya al'adarsa ce, ga shi kuwa, yana bin Shari'ar daidai, ba sai yă kāshe ka ba, kai da kake da Shari'a a rubuce da kuma kaciya, amma kana keta Shari'ar? 28Gama Bayahude na ainihi ba mutum ne wanda yake Bayahude bisa siffar jikinsa na fili ba, kaciya ta ainihi kuwa ba kaciya ce ta fili ta fatar jiki ba. 29#M.Sh 30.6 Wanda yake Bayahude a zuci, ai, shi ne Bayahude. Kaciyar ainihi kuwa a zuci take, wato ta ruhu, ba ta zahiri ba. Irin wannan mutum, Allah ne yake yaba masa, ba ɗan adam ba.
Currently Selected:
Rom 2: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979