Rom 16
16
Gaisuwa
1Ga 'yar'uwarmu Fibi ina sada ku da ita, ita ma kuwa mai hidimar ikilisiya ce a Kankiriya. 2Ku karɓe ta da hannu biyu biyu saboda Ubangiji, ta halin da ya dace da tsarkaka. Ku kuma taimake ta da duk irin abin da ta nemi taimako a gare ku, domin ita ma tā taimaki mutane da yawa, har ma da ni kaina.
3 #
A.M 18.2
Ku gai da Bilkisu da Akila, abokan aikina a cikin Almasihu Yesu, 4waɗanda suka kasai da ransu saboda ni, ba kuwa ni kaɗai nake gode musu ba, har ma da dukkan ikilisiyoyin al'ummai. 5Ku kuma gai da ikilisiyar da take taruwa a gidansu. Ku gai da ƙaunataccena Abainitas, wanda yake shi ne ya fara bin Almasihu a ƙasar Asiya. 6Ku gai da Maryamu, wadda ta yi muku aiki ƙwarai da gaske. 7Ku gai da Andaranikas da Yuniyas, 'yan'uwana, abokan ɗaurina, waɗanda suke shahararru a cikin manzanni, har ma sun riga ni bin Almasihu. 8Ku gai da Amfiliyas, ƙaunataccena a cikin Ubangiji. 9Ku gai da Urbanas abokin aikinmu a cikin Almasihu, da kuma ƙaunataccena Istakis. 10Ku kuma gai da Abalis, amintaccen nan a cikin Almasihu. Ku gai da jama'ar Aristobulus. 11Ku gai da 'dan'uwana Hirudiyan. Ku gai da waɗanda suke na Ubangiji a cikin jama'ar Narkisas. 12Ku gai da Tarafina da Tarafusa, masu aikin Ubangiji. Ku gai da Barsisa, ƙaunatacciya, wadda ta yi aikin Ubangiji ƙwarai da gaske. 13#Mar 15.21Ku gai da Rufas, fitaccen mai bin Ubangiji, da kuma mahaifiyarsa, tawa kuma. 14Ku gai da Asinkiritas, da Filiguna, da Hamisa, da Baturobas, da Hamasa, da kuma 'yan'uwan da suke tare da su. 15Ku gai da Filulugusa, da Yuliya, da Niriyas, da 'yar'uwarsa, da Ulumfas da kuma dukan tsarkakan da suke tare da su. 16Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba. Dukan ikilisiyoyin Almasihu suna gaishe ku.
17Ina roƙonku, 'yan'uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su. 18Ai, irin waɗannan mutane ba sa bauta wa Ubangijinmu Almasihu, sai dai cikinsu. Ta romon kunne da daɗin baki suke yaudarar masu sauƙin kai. 19Amma ku kam, ai, kowa ya san biyayyarku, shi ya sa nake farin ciki da ku. Sai dai ina so ku gwanance da abin da yake nagari, amma ya zama ba ruwanku da mugunta. 20Allah mai ba da salama kuwa, zai sa ku tattake Shaiɗan da hanzari. Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku.
21 #
A.M 16.1
Timoti, abokin aikina, yana gaishe ku, haka kuma Lukiyas da Yason da kuma Susibataras, 'yan'uwana.
22Ni Tartiyas, mai rubuta wasiƙar nan, ina gaishe ku saboda Ubangiji.
23 #
A.M 19.29; 1Kor 1.14;
2Tim 4.20
Gayus, mai masaukina, mai kuma saukar da dukan 'yan ikilisiya, yana gaishe ku. Arastas, ma'ajin gari, da kuma ɗan'uwanmu Kawartas, suna gaishe ku. 24Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku duka. Amin, Amin.
Ƙarasawa da Yabo
25Ɗaukaka tă tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga wa'azin Yesu Almasihu, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun fil'azal. 26Asirin nan kuwa sanar da shi ga dukan al'ummai, ta wurin littattafan annabawa, bisa ga umarnin Allah Madawwami, domin a jawo su, su gaskata, su yi biyayya. 27Ɗaukaka tă tabbata har abada ga Allah Makaɗaicin hikima ta wurin Yesu Almasihu! Amin, Amin.
Currently Selected:
Rom 16: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979