YouVersion Logo
Search Icon

Rom 16:25-27

Rom 16:25-27 HAU

Ɗaukaka tă tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga wa'azin Yesu Almasihu, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun fil'azal. Asirin nan kuwa sanar da shi ga dukan al'ummai, ta wurin littattafan annabawa, bisa ga umarnin Allah Madawwami, domin a jawo su, su gaskata, su yi biyayya. Ɗaukaka tă tabbata har abada ga Allah Makaɗaicin hikima ta wurin Yesu Almasihu! Amin, Amin.