W.Yah 18
18
Faɗuwar Babila Mai Girma
1Bayan haka, na ga wani mala'ika yana saukowa daga Sama, mai iko da yawa, sai aka haskaka duniya da ɗaukakarsa. 2#Ish 21.9; Irm 51.8; W.Yah 14.8; Ish 13.21; Irm 50.39 Sai ya yi kira da murya mai ƙarfi, ya ce,
“Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi!
Ta zama mazaunin aljannu,
Matattarar kowane baƙin aljani,
Da kowane irin ƙazamin tsuntsu, abin ƙyama.
3 #
Ish 23.17; Irm 51.7 Dukkan al'ummai sun yi tsananin jarabar yin fasikanci da ita,
Sarakunan duniya kuma sun yi fasikanci da ita,
Attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”
4 #
Ish 48.20; Irm 50.8; 51.6,45 Sai na ji wata murya daga Sama, tana cewa,
“Ku fito daga cikinta, ya ku jama'ata,
Kada zunubanta su shafe ku,
Kada bala'inta ya taɓa ku.
5 #
Far 18.20,21; Irm 51.9 Domin zunubanta sun yi tsororuwa, sun kai har Sama,
Allah kuwa ya tuna da laifofinta.
6 #
Zab 137.8; Irm 50.29 Ku saka mata daidai da yadda ta yi,
Ku biya ta ninkin ayyukanta,
Ku dama mata biyun abin da ta dama muku.
7 #
Ish 47.7-9
Yadda ta ɗaukaka kanta, ta yi almubazzaranci,
Haka ku ma ku saka mata da azaba, da baƙin ciki gwargwadon haka.
Tun da yake a birnin zuciyarta ta ce, ‘Ni sarauniya ce, a zaune nake,
Ni ba gwauruwa ba ce,
Ba ni da baƙin ciki kuma har abada!’
8Saboda haka, bala'inta zai aukar mata rana ɗaya,
Mutuwa, da baƙin ciki, da yunwa.
Za a kuma ƙone ta,
Domin Ubangiji Allah da yake hukunta ta Mai Ƙarfi ne.”
9 #
Eze 26.16,17 Sarakunan duniya kuma da suka yi fasikanci da zaman almubazzaranci da ita, za su yi mata kuka da kururuwa, in sun ga hayaƙin ƙunarta, 10za su tsaya a can nesa, don tsoron azabarta, su ce,
“Kaitonka! Kaitonka, ya kai babban birni!
Ya kai birni mai ƙarfi, Babila!
A sa'a ɗaya hukuncinka ya auko.”
11 #
Eze 27.31,36 Attajiran duniya kuma suna yi mata kuka suna baƙin ciki, tun da yake, ba mai ƙara sayen kayansu, 12#Eze 27.12,13,22 wato, zinariya, da azurfa, da duwatsun alfarma, da lu'ulu'u, da lallausan lilin, da hajja mai ruwan jar garura, da siliki, da jan alharini, da itacen ƙanshi iri iri, da kayan hauren giwa iri iri, da kayan da aka sassaƙa da itace mai tsada, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na dutse mai sheƙi, 13da kirfa, da kayan yaji, da turaren wuta, da mur, da lubban, da ruwan inabi, da mai, da garin alkama, da alkama, da shanu, da tumaki, da dawaki, da kekunan doki, da kuma bayi, wato, rayukan 'yan adam.
14“Amfanin da kika ƙwallafa rai a kai, har ya kuɓuce miki,
Kayan annashuwarki da na adonki sun ɓace miki, ba kuwa za a ƙara samunsu ba har abada!”
15 #
Eze 27.31,36 Attajiran waɗannan hajjoji da suka arzuta a game da ita, za su tsaya a can nesa don tsoron azabarta, suna kuka, suna baƙin ciki, suna cewa,
16“Kaito! Kaiton babban birnin nan!
Wanda dā ya sa lallausan lilin, da tufafi masu ruwan jar garura, da kuma jan alharini,
Wanda ya ci ado da kayan zinariya, da duwatsun alfarma, da lu'ulu'u!
17 #
Ish 23.14; Eze 27.26-30 Domin a sa'a ɗaya duk ɗumbun dukiyar nan ta hallaka.”
Sai duk masu jiragen ruwa, da masu shiga, da masu tuƙi, da duk waɗanda cinikinsu ya gamu da bahar, suka tsaya a can nesa, 18#Eze 27.32 suna kururuwa da suka ga hayaƙin ƙunarsa, suna cewa,
“Wane birni ne ya yi kama da babban birnin nan?”
19 #
Eze 27.30-34
Har suka tula wa kansu ƙasa suna ta kuka, suna baƙin ciki, suna kururuwa, suna cewa,
“Kaito! Kaiton babban birnin nan!
Wanda duk masu jiragen ruwa a bahar suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa,
A sa'a ɗaya ya hallaka.
20 #
M.Sh 32.43; Irm 51.48 Ki yi farin ciki saboda an yi masa haka, ya sama!
Ku yi farin ciki, ku tsarkaka da manzanni da annabawa, domin Allah ya rama muku abin da ya yi muku!”
21 #
Irm 51.63,64;
Eze 26.21
Sai wani ƙaƙƙarfan mala'ika ya ɗauki wani dutse kamar babban dutsen niƙa, ya jefa a teku, ya ce,
“Haka za a fyaɗa Babila babban birni, da ƙarfi, ba kuwa za a ƙara ganinta ba.
22 #
Eze 26.13; Ish 24.8 #
Irm 7.34; 25.10 Ba za a ƙara jin kiɗan masu molo, da mawaƙa, da masu sarewa, da masu bushe-bushe a cikinki ba,
Ba kuma za a ƙara ganin mai kowace irin sana'a a cikinki ba,
Ba kuma za a ƙara jin niƙa a cikinki ba,
23Fitila ba za ta ƙara haskakawa a cikinki ba,
Ba kuma za a ƙara jin muryar ango da amarya a cikinki ba,
Don attajiranki, dā su ne ƙusoshin duniya,
An kuma yaudari dukkan al'ummai da sihirinki.
24 #
Irm 51.49
Har an tarar hakkin jinin annabawa da na tsarkaka suna a wuyanta, da kuma na duk waɗanda aka kashe a duniya.”
Currently Selected:
W.Yah 18: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979