W.Yah 10
10
Mala'ika da Ƙaramin Littafi
1Sa'an nan na ga wani ƙaƙƙarfan mala'ika yana saukowa daga sama, lulluɓe da gajimare, da bakan gizo a bisa kansa, fuskarsa kamar rana, ƙafafunsa kuma kamar ginshiƙan wuta. 2Ga wani ƙaramin littafi a buɗe a hannunsa. Sai ya tsai da ƙafarsa ta dama a kan teku, ƙafarsa ta hagu kuwa a kan ƙasa, 3ya yi kira da murya mai ƙarfi, kamar zaki yana ruri. Da ya yi kiran, sai aradun nan bakwai suka yi tsawa. 4Sa'ad da kuwa aradun nan bakwai suka yi tsawa, kamar zan rubuta, sai na ji wata murya daga sama tana cewa, “Rufe abin da aradun nan bakwai suka faɗa, kada ka rubuta.” 5#Fit 20.11; M.Sh 32.40; Dan 12.7; Amos 3.7 Sai mala'ikan nan da na gani a tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama, 6ya rantse da wanda yake a raye har abada abadin, wanda ya halicci sama da abin da take a cikinta, da ƙasa da abin da take a cikinta, da kuma teku da abin da take a cikinta, cewa ba sauran wani jinkiri kuma, 7sai dai a lokacin busa ƙahon da mala'ika na bakwai zai busa ne, za a cika asirtaccen nufin nan na Allah, bisa ga bisharar da ya yi wa bayinsa annabawa.
8 #
Eze 2.8—3.3
Sa'an nan muryar nan da na ji daga sama ta sāke yi mini magana, ta ce, “Je ka, ka ɗauki littafin nan da yake a buɗe a hannun mala'ikan da yake a tsaye a bisa teku da ƙasa.” 9Sai na je wurin mala'ikan, na ce masa, ya ba ni ƙaramin littafin. Sai ya ce mini, “Karɓi ka cinye, zai yi maka ɗaci a ciki, amma a baka kamar zuma yake don zaƙi.” 10Sai na karɓi ƙaramin littafin daga hannun mala'ikan, na cinye. Sai ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma da na cinye, cikina ya ɗau ɗaci. 11Sai kuma aka ce mini, “Lalle ne ka sāke yin annabci a game da jama'a iri iri, da al'ummai, da harsuna, da kuma sarakuna da yawa.”
Currently Selected:
W.Yah 10: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979