Zab 73
73
LITTAFI NA UKU
(Zab 73—89)
Ƙarshen Mugaye
1Hakika, Allah yana yi wa Isra'ila alheri,
Da waɗanda suke da tsarkin zuciya!
2Amma ina gab da fāɗuwa,
Ƙafafuna sun kusa zamewa,
3Saboda na ji kishin masu girmankai,
Sa'ad da na ga mugaye suna arziki.
4Ba su jin zafin ciwo,
Su ƙarfafa ne, lafiyayyu.
5Ba su shan wahala yadda sauran mutane suke sha,
Ba su da wahala kamar sauran mutane,
6Don haka suka ɗaura girmankai kamar dutsen wuya,
Suka sa hargitsi kuma kamar riga.
7Zuciyarsu, cike take da mugunta,
Tunaninsu kuma cike suke da mugayen ƙulle-ƙulle.
8Sukan yi wa waɗansu ba'a,
Suna faɗar mugayen abubuwa,
Masu girmankai ne su, suna shawara
A kan yadda za su zalunci waɗansu.
9Sukan faɗi baƙar magana a kan Allah na Sama,
Su ba da umarnai na girmankai ga mutane a duniya,
10Har jama'ar Allah ma sukan koma wurinsu,
Suna ɗokin gaskata dukan abin da suke faɗa musu.
11Sukan ce, “Ai, Allah ba zai sani ba,
Maɗaukaki ba zai bincika ba!”
12Haka mugaye suke.
Suna da dukiya da yawa, amma sai ƙaruwa suke ta yi.
13Ashe, a banza nake kiyaye kaina da tsarki,
Hannuwana kuma a tsabtace daga zunubi?
14Ya Allah, ka sa ina shan wahala dukan yini,
Kana horona kowace safiya!
15Da na faɗi waɗannan abubuwa,
Da na zama marar gaskiya ga jama'arka.
16Don haka na yi iyakar ƙoƙari in fahimci wannan,
Ko da yake ya cika wuya,
17Sai sa'ad da na shiga Haikalinka,
Sa'an nan na fahimci abin da zai sami mugaye.
18Hakika ka sa su a wurare masu santsi,
Ka sa su su fāɗi su hallaka sarai!
19Cikin ƙyaftawar ido aka hallaka su,
Suka yi mummunan ƙarshe!
20Ya Ubangiji, kamar mafarki suke
Wanda akan manta da shi da safe,
Sa'ad da mutum ya farka yakan manta da kamanninsa.
21Sa'ad da zuciyata ta ɓaci,
Hankalina ya tashi,
22Sai na zama wawa, ban fahimta ba,
Na nuna halin dabba a gabanka.
23Duk da haka ina tare da kai kullayaumin,
Kana riƙe da hannuna.
24Shawararka, tana bi da ni,
Daga ƙarshe kuma za ka karɓe ni da daraja.
25In banda kai, wa nake da shi a Sama?
Tun da yake ina da kai, me kuwa nake bukata a duniya?
26Kwanyata da jikina za su raunana,
Amma Allah ne ƙarfina,
Shi nake so har abada!
27Hakika waɗanda za su rabu da kai za su mutu,
Za ka hallakar da marasa aminci gare ka.
28Amma a gare ni, ya fi mini kyau, in kasance kusa da Allah!
Na sami mafaka a wurin Ubangiji Allah,
Da zan yi shelar dukan abin da ya aikata.
Currently Selected:
Zab 73: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979