Bible App logo
Search Icon

Zab 72

72
Mulkin Sarki Mai Adalci
1Ka koya wa sarki ya yi shari'a
Da adalcinka, ya Allah,
Ka kuma ba shi shari'arka,
2Don ya yi mulkin jama'arka bisa kan shari'a,
Ya kuma bi da mulki da adalci.
3Ka sa ƙasar ta mori wadatarta,
Ka sa al'ummar ta san adalci.
4Ka sa sarki ya yi wa talakawa shari'ar gaskiya,
Ya taimaki waɗanda suke da bukata,
Ya kuma hukunta azzalumai!
5Ka sa su girmama ka
Muddin rana tana haskakawa,
Muddin wata yana ba da haske dukan lokaci.
6Ka sa sarki ya zama kamar ruwan sama a gonaki,
Ya zama kamar yayyafi a bisa ƙasa.
7Ka sa adalci ya bunƙasa a zamaninsa,
Wadata ta dawwama muddin wata na haskakawa.
8 # Zak 9.10 Mulkinsa ya kai daga teku zuwa teku,
Daga Kogin Yufiretis, har zuwa iyakar duniya.
9Kabilan hamada za su durƙusa a gabansa,
Abokan gābansa za su kwanta warwar a cikin ƙura.
10Sarakunan Esbanya da na tsibirai,
Za su ba shi kyautai,
Sarakunan Arabiya da na Habasha
Za su kawo masa kyautai.
11Dukan sarakuna za su durƙusa a gabansa,
Dukan sauran al'umma za su bauta masa!
12Yakan ceci matalauta waɗanda suka yi kira gare shi,
Da waɗanda suke da bukata,
Da waɗanda ba a kula da su.
13Yakan ji tausayin gajiyayyu da matalauta,
Yakan ceci rayukan waɗanda suke da bukata.
14Yakan cece su daga zalunci da kama-karya,
Rayukansu suna da daraja a gare shi.
15Ran sarki yă daɗe!
Da ma a ba shi zinariya daga Arabiya,
Da ma a yi masa addu'a dukan lokaci,
Allah ya sa masa albarka kullum!
16Da ma a sami hatsi mai yawa a ƙasar,
Da ma amfanin gona yă cika tuddan,
Yă yi yawa kamar itatuwan al'ul na Lebanon,
Da ma birane su cika da mutane,
Kamar ciyayin da suke girma a sauruka.
17Da ma a yi ta tunawa da sunansa har abada,
Da ma shahararsa ta ɗore muddin rana tana haskakawa.
Da ma dukan sauran al'umma su yabi sarkin,
Dukan jama'a su roƙi Allah yă sa musu albarka,
Kamar yadda ya sa wa sarki albarka.
18Ku yabi Ubangiji, Allah na Isra'ila,
Wanda shi kaɗai ne yake aikata al'amuran nan masu banmamaki!
19Ku yabi sunansa mai daraja har abada,
Allah ya sa ɗaukakarsa ta cika dukan duniya!
Amin! Amin!
20Ƙarshen addu'o'in Dawuda, ɗan Yesse ke nan.

Currently Selected:

Zab 72: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in