Zab 69
69
Kukan Neman Taimako
1Ka cece ni, ya Allah!
Ruwa ya sha kaina.
2Ina nutsewa cikin laka mai zurfi,
Ba kuwa ƙasa mai ƙarfi,
Na tsunduma cikin ruwa mai zurfi,
Raƙuman ruwa kuwa sun kusa kashe ni.
3Na gaji da kira, ina neman taimako,
Maƙogwarona yana yi mini ciwo,
Idanuna duka sun gaji,
Saboda ina zuba ido ga taimakonka.
4 #
Zab 35.19; Yah 15.25 Waɗanda suke ƙina ba dalili
Sun fi gashin kaina yawa,
Waɗanda suke baza ƙarya suke ƙina,
Suna da ƙarfi, suna kuwa so su kashe ni.
Suka tilasta ni in mayar da abubuwan da ba satarsu na yi ba.
5Zunubaina ba a ɓoye suke a gare ka ba ya Allah,
Ka san irin wawancin da na yi!
6Kada ka bar ni in jawo kunya ga waɗanda suka dogara gare ka,
Ya Ubangiji Allah Mai Iko Dukka!
Kada ka bar ni in jawo abin kunya
Ga waɗanda suke maka sujada, ya Allah na Isra'ila!
7Sabili da kai ne aka ci mutuncina,
Kunya ta rufe ni.
8Kamar baƙo nake ga 'yan'uwana,
Haka ma ga iyalina, kamar baƙo nake.
9 #
Yah 2.17;
Rom 15.3
Ƙaunar da nake da ita ta yin ibada a Haikalinka
Tana iza ni a ciki kamar wuta,
Zargin da suke yi a kanka, ya fāɗa a kaina.
10Na ƙasƙantar da kaina ta wurin yin azumi,
Jama'a kuwa suka ci mutuncina.
11Na sa tufafin makoki,
Sai suka maishe ni abin dariya.
12A tituna suna ta magana a kaina,
Bugaggu da giya kuwa suna raira waƙa a kaina.
13Amma ni, zan yi addu'a gare ka, ya Ubangiji,
Ka amsa mini, ya Allah, a lokacin da ka zaɓa,
Sabili da muhimmiyar ƙaunarka,
Saboda kana cika alkawarinka na yin ceto.
14Ka cece ni daga nutsewa cikin wannan laka,
Ka kiyaye ni daga maƙiyana,
Daga kuma wannan ruwa mai zurfi.
15Kada ka bar ambaliyar ruwa ta rufe ni.
Kada ka bar ni in mutu cikin zurfafa,
Ko in nutse a cikin kabari.
16Sabili da madawwamiyar ƙaunarka, ka amsa mini, ya Ubangiji,
Ka juyo wurina, saboda juyayinka mai girma!
17Kada ka ɓoye kanka daga bawanka,
Ina shan babbar wahala, ka yi hanzari ka amsa mini!
18Ka zo ka fanshe ni,
Ka kuɓutar da ni daga abokan gābana.
19Ka san yadda ake cin mutuncina,
Da yadda ake kunyata ni, ake ƙasƙantar da ni,
Kana ganin dukan abokan gābana.
20Zuciyata ta karai saboda cin mutuncin da ake ci mini,
Ni kuwa ba ni da mataimaki,
Na sa zuciya za a kula da ni,
Amma babu.
Na sa zuciya zan sami ta'aziyya,
Amma ban samu ba.
21 #
Mat 27.48; Mar 15.36; Luk 23.26; Yah 19.28,29 Sa'ad da na ji yunwa, sai suka ba ni dafi,
Sa'ad da na ji ƙishi, sai suka ba ni ruwan tsami.
22 #
Rom 11.9,10 Allah ya sa bukukuwansu su zama lalacewarsu,
Shagulgulansu kuma su zama sanadin fāɗuwarsu!
23Ka makantar da su, har da ba za su iya gani ba,
Kullum ka sa bayansu ya ƙage!
24Ka kwarara musu fushinka,
Bari zafin fushinka ya ci musu!
25 #
A.M 1.20
Allah ya sa su gudu su bar sansaninsu,
Kada wani ya ragu da rai cikin alfarwansu!
26Sun tsananta wa waɗanda ka hukunta,
Suna taɗin shan wuyar waɗanda ka aukar wa cutar.
27Ka riɓaɓɓanya zunubansu,
Kada ka bar su su sami rabon kome daga cikin cetonka.
28 #
Fit 32.32; W.Yah 3.5; 13.8; 17.8 Ka sa a goge sunansu daga cikin littafin rai,
Kada a sa su a lissafin jama'arka.
29Amma ni mai bukata ne, ina shan wahala,
Ka tsame ni, ya Allah, ka cece ni!
30Zan raira waƙar yabo ga Allah,
Zan yi shelar girmansa ta wurin yi masa godiya,
31Wannan zai daɗaɗa wa Ubangiji rai
Fiye da hadayar bijimi,
Fiye da a ba shi bijimi bana bakwai.
32Sa'ad da masu bukata suka ga wannan za su yi murna,
Waɗanda suke yi wa Allah sujada kuwa za a ƙarfafa su.
33Ubangiji yana kasa kunne ga masu bukata,
Bai manta da jama'arsa da suke a kurkuku ba.
34Ku yabi Allah, ku al'arshi da duniya, ku yabi Allah,
Tekuna da dukan talikan da suke cikinsu!
35Gama zai ceci Sihiyona,
Ya sāke gina garuruwan Yahuza,
Jama'arsa za su zauna a wurin, su mallaki ƙasar.
36Zuriyar bayinsa za su gāje ta,
Masu ƙaunarsa za su zauna a wurin.
Currently Selected:
Zab 69: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

:
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979