Zab 64
64
Addu'ar Neman Tsari
1Ina shan wahala, ya Allah, ka ji addu'ata!
Ina jin tsoro, ka cece ni daga maƙiyana!
2Ka kiyaye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye,
Da iskancin mugayen mutane.
3Sukan wasa harsunansu kamar takuba,
Sukan kai bāra da mugayen maganganu kamar kibau.
4Sukan yi kwanto su harbi mutanen kirki da kibau,
Nan da nan sukan yi harbi, ba su kuwa jin tsoro.
5Suna ƙarfafa junansu cikin yin mugayen ƙulle-ƙullensu,
Sukan yi ta taɗi a kan inda za su kafa tarkunansu.
“Ba wanda zai gan mu,” in ji su.
6Sukan shirya maƙarƙashiya, su ce,
“Ai, mun gama shirin aikata laifi sarai.”
Zuciyar mutum da tunaninsa, suna da wuyar ganewa!
7Amma Allah zai harbe su da kibansa,
Za a yi musu rauni nan da nan.
8Zai hallaka su saboda maganganunsu,
Duk wanda ya gan su zai kaɗa kansa.
9Dukansu za su ji tsoro,
Za su faɗi abin da Allah ya aikata,
Su yi tunani a kan ayyukansa.
10Dukan masu adalci za su yi murna,
Saboda abin da Ubangiji ya aikata.
Za su sami mafaka a gare shi,
Dukan mutanen kirki za su yabe shi.
Currently Selected:
Zab 64: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979