Zab 53
53
Muguntar Mutane
(Zab 14.1-7)
1 #
Rom 3.10-12
Wawaye sukan ce wa kansu, “Ba Allah.”
Dukansu sun lalace, sun aikata mugayen al'amura,
Ba wanda yake aikata abin da yake daidai.
2Daga Sama Allah ya dubi mutane,
Ya ga ko akwai masu hikima
Waɗanda suke yi masa sujada.
3Amma dukansu sun koma baya,
Su duka mugaye ne,
Ba wanda yake aikata abin da yake daidai,
Babu ko ɗaya.
4Allah ya ce, “Ashe, ba su sani ba?
Ashe, mugayen nan jahilai ne?
Ta wurin yi wa jama'ata fashi suke rayuwa,
Ba sa yin addu'a gare ni.”
5Amma sa'an nan za su firgita ƙwarai,
Irin yadda ba su taɓa yi ba,
Gama Allah ya warwatsa ƙasusuwan maƙiyanka.
Ya kore su sarai, saboda ya ƙi su.
6Dā ma ceto ya zo ga Isra'ila daga Sihiyona!
Sa'ad da Allah ya sāke arzuta jama'arsa,
Zuriyar Yakubu za ta yi farin ciki,
Jama'ar Isra'ila kuwa za ta yi murna.
Currently Selected:
Zab 53: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

:
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979