Zab 52
52
Hukuncin Allah da Alherinsa
1Me ya sa kake fariya da muguntarka,
Ya kai, babban mutum?
Ƙaunar Allah tana nan a koyaushe.
2Kana shirya maƙarƙashiya don ka lalatar da waɗansu,
Harshenka kamar aska mai kaifi yake.
Kana ƙirƙiro ƙarairayi kullum.
3Kana ƙaunar mugunta fiye da nagarta,
Kana kuwa ƙaunar faɗar ƙarya fiye da gaskiya.
4Kana jin daɗin cutar mutane da maganganunka,
Ya kai, maƙaryaci!
5Don haka Allah zai ɓata ka har abada,
Zai kama ka, yă jawo ka daga alfarwarka,
Zai kawar da kai daga ƙasar masu rai.
6Adalai za su ga wannan, su ji tsoro,
Za su yi maka dariya, su ce,
7“Duba, ga mutumin da bai dogara ga Allah
Don ya sami zaman lafiyarsa ba.
A maimakon haka, sai ya dogara ga wadatarsa.
Yana neman zaman lafiyarsa ta wurin muguntarsa.”
8Amma ni, kamar itacen zaitun nake, wanda yake girma kusa da Haikalin Allah,
Ina dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa har abada abadin.
9Zan gode maka, ya Ubangiji,
Saboda abin da ka aikata.
Zan dogara gare ka,
Sa'ad da nake sujada tare da jama'arka,
Domin kai mai alheri ne.
Currently Selected:
Zab 52: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979