Zab 42
42
LITTAFI NA BIYU
(Zab 42—72)
Kewar Allah a Baƙuwar Ƙasa
1Kamar yadda kishimi yake marmarin ruwan sanyi daga rafi,
Haka nake marmarinka, ya Allah.
2Ina jin ƙishinka, ya Allah, ya Allah Mai Rai,
Yaushe zan tafi in yi sujada a gabanka?
3Dare da rana ina kuka,
Hawayena kaɗai su ne abincina,
A kowane lokaci maƙiyana suna ta tambayata,
“Ina Allahnka?”
4Zuciyata takan ɓaci in na tuna da abin da ya wuce,
Sa'ad da nakan tafi tare da taron jama'a zuwa Haikalin Allah,
Ina bishe su a jere.
Taron jama'a masu farin ciki, suna raira waƙa,
Suna ta da murya, suna yabon Allah.
5Me ya sa nake baƙin ciki haka?
Me ya sa nake damuwa ƙwarai?
Zan dogara ga Allah,
Zan sāke yin yabonsa,
Mai Cetona, Allahna.
6Zuciyata ta karai
Saboda haka zan tuna da kai
A wajen Urdun, da kusa da Dutsen Harmon, da na Mizar,
Zan tuna da kai.
7Zurfafan tekuna suna kiran junansu,
Matsirgar ruwa na Allah kuwa suna ta ruri!
Igiyoyin ruwa na baƙin ciki
Suka yi wa raina ambaliya.
8Ubangiji ya nuna madawwamiyar ƙaunarsa kowace rana!
Ni ma in raira yabo gare shi kowane dare,
In yi addu'a ga Allah, wanda ya ba ni rai.
9Ga Allah wanda yake tsarona na ce,
“Me ya sa ka manta da ni?
Me ya sa nake ta shan wahala
Saboda muguntar maƙiyana?”
10An ragargaza ni da zargin maƙiyana
Waɗanda suke tambayata kullum,
“Ina Allahnka?”
11Me ya sa ni ɓacin rai haka?
Me ya sa ni damuwa?
Zan dogara ga Allah.
Har yanzu ma zan yabe shi,
Mai Cetona, Allahna.
Currently Selected:
Zab 42: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

:
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979