Zab 40
40
Wakar Yabo
1Na yi ta jiran taimakon Ubangiji,
Sa'an nan ya kasa kunne gare ni, ya ji kukana.
2Ya fisshe ni daga rami mai hatsari!
Ya aza ni a kan dutse lafiya lau.
Ya kawar mini da tsoro.
3Ya koya mini raira sabuwar waƙa,
Waƙar yabon Allahnmu.
Da yawa idan suka ga wannan za su tsorata,
Za su kuwa dogara ga Ubangiji.
4Mai farin ciki ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,
Wanda bai juya ga gumaka ba,
Ko ya haɗa kai da masu sujada ga allolin karya.
5Ka yi mana abubuwa masu yawa, ya Ubangiji Allahna.
Ba wani kamarka!
Idan na yi ƙoƙari in faɗe su duka,
Sun fi ƙarfin in faɗa.
6 #
Ibr 10.5-7
Ba ka bukatar baye-baye da hadayu,
Ba ka so a miƙa maka hadayun ƙonawa
Na dabbobi a bisa bagade ba,
Ko baya-baye don a kawar da zunubai.
A maimakon haka, ka ba ni kunnuwan da zan saurare ka.
7Sai na amsa, “Ga ni, umarnanka zuwa gare ni
Suna a Littafin Shari'a.
8Ina ƙaunar in aikata nufinka sosai, ya Allah!
Ina riƙe da koyarwarka a zuciyata.”
9A taron dukan jama'arka, ya Ubangiji,
Na ba da albishir na cetonka.
Ka sani ba zan fasa hurta shi ba.
10Ban riƙe labarin cetonka don kaina kaɗai ba,
Nakan yi maganar amincinka, da taimakonka a koyaushe.
Ba na yin shiru a taron dukan jama'arka,
Amma ina ta shaida madawwamiyar ƙaunarka da amincinka.
11Ya Ubangiji, na sani ba za ka fasa yi mini jinƙai ba!
Ƙaunarka da amincinka za su kiyaye lafiyata kullum.
12Wahalai iri iri sun kewaye ni, har ba su ƙidayuwa!
Alhakin zunubaina ya tarar da ni,
Har ba na iya gani,
Sun fi gashin kaina yawa, na karaya.
13Ka cece ni, ya Allah,
Ya Ubangiji, ka yi hanzari ka taimake ni!
14Ka sa masu so su kashe ni,
A ci nasara a kansu, su ruɗe!
Ka sa waɗanda suke murna saboda wahalaina
Su koma baya, su sha kunya!
15Ka sa waɗanda suke mini ba'a
Su razana sabili da faɗuwarsu!
16Ka sa dukan waɗanda suke zuwa gare ka
Su yi murna, su yi farin ciki!
Ka sa waɗanda suke ƙaunar cetonka
Kullayaumi su ce, “Allah da girma yake!”
17Ba ni da ƙarfi, ba mataimaki,
Ya Allah, ka zo wurina da hanzari.
Kai ne mataimakina da Mai Cetona,
Kada ka yi jinkiri, ya Ubangiji!
Currently Selected:
Zab 40: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979