Zab 29
29
Muryar Ubangiji a cikin Hadiri
1 #
Zab 96.7-9
Ku yabi Ubangiji, ku alloli,
Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa.
2Ku yabi sunan Ubangiji mai daraja,
Ku rusuna a gaban Mai Tsarki sa'ad da ya bayyana.
3An ji muryar Ubangiji a kan tekuna,
Allah Maɗaukaki ya yi tsawa,
Tsawar muryarsa kuwa ta yi amsa kuwa a bisa teku.
4An ji muryar Ubangiji
A dukan ikonsa da zatinsa!
5Muryar Ubangiji takan karya itatuwan al'ul,
Har ma da itatuwan al'ul na Lebanon.
6Yakan sa duwatsun Lebanon su yi tsalle kamar 'yan maruƙa,
Ya kuma sa Dutsen Harmon ya yi tsalle kamar ɗan maraƙi.
7Muryar Ubangiji ta sa walƙiya ta walƙata.
8Muryarsa ta sa hamada ta girgiza,
Ta girgiza hamadar Kadesh.
9Muryar Ubangiji ta sa barewa ta haihu,
Ta sa itatuwa su kakkaɓe,
Sa'ad da aka yi sowa a cikin Haikalinsa,
Aka ce, “Daukaka ga Allah!”
10Ubangiji yana sarautar ruwa mai zurfi,
Yana sarauta kamar sarki har abada.
11Ubangiji yana ba jama'arsa ƙarfi,
Ya sa musu albarka da salama.
Currently Selected:
Zab 29: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979