Zab 21
21
Yabo saboda Nasara
1Sarki yana murna, ya Ubangiji,
Domin ka ba shi ƙarfi,
Yana cike da farin ciki,
Don ka sa ya ci nasara.
2Ka biya masa bukatarsa,
Ka amsa roƙonsa.
3Ka zo gare shi da albarka mai yawa,
Ka sa kambin zinariya a kansa.
4Ya roƙi rai, ka kuwa ba shi mai tsawo,
Da yawan kwanaki.
5Darajarsa tana da girma saboda taimakonka,
Ka sa ya yi suna da martaba.
6Albarkarka tana a kansa har abada,
Kasancewarka tare da shi, takan cika shi da murna.
7Sarki yana dogara ga Maɗaukaki,
Saboda madawwamiyar ƙaunar Ubangiji
Zai zama sarki har abada.
8Sarki zai kakkama dukan magabtansa,
Zai kakkama duk waɗanda suke ƙinsa.
9Ubangiji zai hallaka su kamar harshen wuta, sa'ad da ya bayyana.
Ubangiji zai cinye su a cikin fushinsa,
Wuta kuma za ta cinye su ƙurmus.
10Sarki zai karkashe 'ya'yansu duka,
Zai yanyanke dukan zuriyarsu.
11Sun ƙulla mugayen dabaru, suna fakonsa,
Amma ba za su yi nasara ba.
12Zai harba kibansa a kansu,
Ya sa su juya su gudu.
13Ya Ubangiji, ka zo da ƙarfinka!
Za mu raira waƙa mu yabi ikonka.
Currently Selected:
Zab 21: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979