YouVersion Logo
Search Icon

Zab 145

145
Waƙar Yabon Allah domin Alherinsa da Ikonsa
1Zan yi shelar girmanka, ya Allahna, Sarkina,
Zan yi maka godiya har abada abadin.
2Kowace rana zan yi maka godiya,
Zan yabe ka har abada abadin.
3Ubangiji mai girma ne, dole ne a fifita yabonsa,
Girmansa ya fi ƙarfin ganewa.
4Za a yabi abin da ka aikata daga tsara zuwa tsara,
Za su yi shelar manya manyan ayyukanka.
5Mutane za su yi magana a kan darajarka da ɗaukakarka,
Ni kuwa zan yi ta tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.
6Mutane za su yi magana a kan manya manyan ayyukanka,
Ni kuwa zan yi shelar girmanka.
7Za su ba da labarin girmanka duka,
Su kuma raira waƙa a kan alherinka.
8Ubangiji mai ƙauna ne, mai jinƙai, mai jinkirin fushi,
Cike da madawwamiyar ƙauna.
9Shi mai alheri ne ga kowa,
Yana juyayin dukan abin da ya halitta.
10Ya Ubangiji, talikanka duka za su yabe ka,
Jama'arka kuma za su yi maka godiya!
11Za su yi maganar darajar mulkinka,
Su ba da labarin ikonka,
12Domin haka dukan mutane za su san manyan ayyukanka,
Da kuma darajar ɗaukakar mulkinka.
13Mulkinka, madawwamin mulki ne,
Sarki ne kai har abada.
14Ubangiji, yakan taimaki dukan waɗanda yake shan wahala,
Yakan ta da waɗanda aka wulakanta.
15Dukan masu rai suna sa zuciya gare shi,
Yana ba su abinci a lokacin da suke bukata,
16Yana kuwa ba su isasshe,
Yakan biya bukatarsu duka.
17Ubangiji mai adalci ne a abin da yake yi duka,
Mai jinƙai ne a ayyukansa duka.
18Yana kusa da dukan waɗanda suke kira gare shi,
Waɗanda suke kiransa da zuciya ɗaya.
19Yakan biya bukatar dukan waɗanda suke tsoronsa,
Yakan ji kukansu, ya cece su.
20Yakan kiyaye dukan waɗanda suke ƙaunarsa,
Amma zai hallaka mugaye duka.
21A kullum zan yabi Ubangiji,
Bari talikai duka su yabi sunansa mai tsarki har abada!

Currently Selected:

Zab 145: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in