K.Mag 9
9
Hikima da Dakikanci
1Hikima ta gina gidanta, ta yi masa ginshiƙai bakwai. 2Ta sa an yanka dabba don biki, ta gauraya ruwan inabi da kayan yaji, ta shirya tebur. 3Ta aiki barorinta 'yan mata su je su hau wuri mafi tsayi a birni su yi kira. 4“Ku shigo, ku jahilai!” Ga dolo kuwa ta ce, 5“Zo ka ci abincina ka sha ruwan inabin da na gauraya. 6Ka rabu da ƙungiyar jahilai, ka rayu, ka bi hanyar ilimi.”
7Idan ka kwaɓi mai fāriya, za ka gamu da cin mutunci, idan ka tsauta wa mugu, kai ne za ka cutu. 8Faufau kada ka kuskura ka kwaɓi mai fāriya, zai ƙi ka saboda wannan, amma idan ka kwaɓi mai hikima zai girmama ka. 9Dukan abin da ka faɗa wa mutum mai hikima, zai ƙara masa hikima. Dukan abin da ka faɗa wa adali zai ƙara masa ilimi.
10 #
Ayu 28.28; Zab 111.10; K.Mag 1.7 Domin ka zama mai hikima dole ka fara da tsoron Ubangiji. Idan ka san Mai Tsarki, ka sami ganewa. 11Hikima za ta ƙara shekarunka. 12Kai ne da riba in ka sami hikima. Kai za ka sha hasara in ka ƙi ta.
13Wawanci kamar mace ce mai kwakwazo, jahila, marar kunya. 14Takan zauna a ƙofar gidanta, ko a wurin da ya fi duka bisa a cikin gari. 15Takan yi ta kiran masu wucewa waɗanda hankalinsu yake a kan ayyukansu, ta ce, 16“Ku shigo, ku jahilai!” Takan ce wa dolo, 17“Ruwan da aka sata ya fi daɗi, haka nan kuma abincin da ake satar ya fi daɗi.” 18Waɗanda suka fāɗa a hannunta ba su sani mutuwa za su yi ba, waɗanda suka riga sun shiga kuwa suna can sun nutse cikin lahira.
Currently Selected:
K.Mag 9: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: