YouVersion Logo
Search Icon

K.Mag 8

8
Yabon Hikima
1 # K.Mag 1.20,21 Ku kasa kunne! Hikima tana kira.
Tana so a ji ta.
2Tana tsaye bisa kan tuddai a bakin hanya
Da a mararraban hanyoyi.
3A ƙofofin shiga birni, tana kira,
4“Ina roƙonku, ya ku, 'yan adam,
Ina kiran kowane mutum da yake a duniya.
5Ba ku balaga ba? To, ku balaga.
Ku wawaye ne? Ku koyi hankali.
6Ku kasa kunne ga jawabina mafi kyau,
Dukan abin da na faɗa muku daidai ne.
7Abin da na faɗa gaskiya ne,
Ƙarairayi abin ƙi ne a gare ni.
8Kowane abu da na faɗa gaskiya ne,
Ba wani abu da yake na laifi ko na ruɗawa.
9Ga mutum mai basira, dukan abu ne a sarari,
Ga wanda aka sanar da shi sosai, abu ne a sawwaƙe.
10Ka zaɓi koyarwata fiye da azurfa,
Ka zaɓi ilimi fiye da zinariya tsantsa.
11“Ni ce hikima, na fi lu'ulu'ai,
Cikin dukan abin da kake so, ba kamata.
12Ni ce hikima, ina da basira,
Ina da ilimi da faɗar daidai.
13Ƙin mugunta shi ne tsoron Ubangiji,
Na ƙi girmankai, da fāriya, da mugayen hanyoyi,
Da maganganu na ƙarya.
14Nakan shirya abin da zan yi, in kuwa yi shi.
Ina da fahimi, ina da ƙarfi.
15Nakan taimaki sarakuna su yi mulki,
Mahukunta kuma su tsara dokoki masu kyau.
16Kowane mai mulki a duniya, da taimakona yake mulki,
Ƙusoshin hukumomi da dattawan gari duka ɗaya.
17Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata,
Dukan wanda yake nemana kuma zai same ni.
18Ina da dukiya da daraja da zan bayar,
Da wadata da nasara kuma.
19Abin da za ka samu daga gare ni
Ya fi zinariya kyau, da azurfa tsantsa.
20A kan hanyar adalci nake tafiya,
Rankai a kan hanyoyin gaskiya.
21Ina ba da dukiya ga waɗanda suke ƙaunata,
Ina kuma cika gidajensu da wadata.
22 # W.Yah 3.14 “Ni ce halittar farko da Ubangiji
Ya fara halittawa daga cikin ayyukansa tuntuni.
23Da farkon farawa ni aka fara halittawa
Kafin a yi duniya.
24Ni aka fara yi kafin tekuna,
A sa'ad da ba maɓuɓɓugan ruwa.
25Ni aka fara yi kafin a yi duwatsu,
Kafin a kafa tuddai a wurarensu,
26Kafin Allah ya halicci duniya da filayenta,
Ko ɗan ɓarɓashin ƙasa.
27A can nake sa'ad da ya shata sararin sama,
Da sa'ad da ya shimfiɗa al'arshi a hayin tekuna,
28Da sa'ad da ya sa gizagizai a sararin sama,
Ya buɗe maɓuɓɓugan teku,
29Ya kuma umarci ruwan teku, kada ya zarce wurin da ya sa.
Ina can sa'ad da ya kafa harsashin ginin duniya.
30Ina kusa da shi kamar mai tsara fasalin gini,
Ni ce abar murnarsa kowace rana,
A ko yaushe ina farin ciki a gabansa.
31Ina farin ciki da duniya,
Ina murna da 'yan adam.
32“Yanzu ku matasa, ku kasa kunne gare ni,
Ku yi abin da na ce, za ku yi farin ciki.
33Ku saurari abin da aka koya muku,
Ku zama masu hikima, kada ku yi sakaci da ita.
34Mutumin da ya kasa kunne gare ni, zai yi farin ciki haka nan,
Wato yakan tsaya a ƙofata ko yaushe,
Yana kuma jira a ƙofar shiga gidana.
35Mutumin da ya same ni ya sami rai,
Ubangiji zai ji daɗinsa.
36Mutumin da bai same ni ba ya cuci kansa,
Duk wanda yake ƙina mutuwa yake ƙauna.”

Currently Selected:

K.Mag 8: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in