K.Mag 2
2
Sakamakon Neman Hikima
1Ɗana, ka koyi abin da nake koya maka, sam kada ka manta da abin da na faɗa maka ka yi. 2Ka kasa kunne ga abin da yake na hikima, ka yi ƙoƙari ka fahimce shi. 3I, ka roƙi ilimi da tsinkaya. 4Ka nema da iyakar ƙoƙarinka kamar yadda za ka nemi azurfa, ko kowace irin ɓoyayyiyar dukiya. 5Idan ka yi za ka san abin da ake nufi da tsoron Ubangiji. Za ka yi nasara a kan koyon sanin Allah. 6Ubangiji ne yake ba da hikima. Ilimi da fahimi kuwa suna cikin kalmominsa. 7Shi yake tanada wa adalai taimako da kiyayewa, wato mutane masu aminci. 8Yakan kiyaye waɗanda suke lura da kyau, ya kiyaye waɗanda suke dogara gare shi.
9Idan ka kasa kunne gare ni za ka san abin da yake daidai, da abin da yake gaskiya, da abin da yake na kirki. Za ka san abin da za ka yi. 10Za ka zama mai hikima, iliminka zai faranta maka rai. 11Tsinkayarka da fahiminka za su tsare ka. 12Za su hana ka aikata mugayen ayyuka, za su nisantar da kai daga mutane masu ta da hargitsi da irin maganganunsu, 13mutane waɗanda suka bar zaman adalci don su zauna cikin duhun zunubi, 14waɗanda suke jin daɗin yin laifi, suna nishaɗi cikin mugunta. 15Ba za a dogara da su ba, ba kuwa za a iya amincewa da su ba.
16Za a nisantar da kai daga mazinaciya, wadda take ƙoƙari ta lalatar da kai da daɗin bakinta, 17marar aminci ga mijinta, wadda ta manta da tsarkakan alkawaran da ta ɗauka. 18Idan ka tafi gidanta ka kama hanyar mutuwa. Tafiya can kama hanyar zuwa lahira ne. 19Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa. Ba zai ƙara komowa ga hanyar rai ba. 20Saboda haka dole ka bi hanyar da mutanen kirki suka bi, ka bi gurbin adalai. 21Mutane adalai, masu kamewa, su ne za su zauna ƙasarmu. 22Amma Allah zai fizge mugaye daga ƙasar, ya kuma tumɓuke masu zunubi kamar yadda ake tumɓuke shuke-shuke daga ƙasa.
Currently Selected:
K.Mag 2: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979