YouVersion Logo
Search Icon

L.Ƙid 27

27
Roƙon 'Ya'yan Zelofehad Mata
1Sai 'ya'yan Zelofehad, mata, ɗan Hefer ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manassa, ɗan Yusufu, suka tafi ƙofar alfarwa ta sujada. Sunayen 'ya'ya, matan ke nan, Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza. 2Da suka tafi, suka tsaya a gaban Musa da Ele'azara, firist, da gaban shugabanni, da dukan taron jama'a, suka ce, 3“Mahaifinmu ya rasu cikin jeji. Ba ya cikin ƙungiyar Kora wadda ta tayar wa Ubangiji. Ya rasu saboda alhakin zunubinsa. Ga shi, ba shi da 'ya'ya maza. 4Don me za a tsame sunan mahaifinmu daga cikin zuriyar iyalinsa saboda ba shi da ɗa? In ka yarda, muna roƙonka ka ba mu gādo tare da 'yan'uwan mahaifinmu.”
5Musa ya kai maganarsu a gaban Ubangiji. 6Ubangiji ya ce wa Musa, 7#L.Ƙid 36.2“Maganar 'ya'yan Zelofehad, mata, daidai ce, saika ba su gādo tare da 'yan'uwan mahaifinsu. Za ka sa gādon mahaifinsu ya zama nasu. 8Sai kuma ka shaida wa Isra'ilawa, ka ce, ‘Idan mutum ya rasu ba shi da ɗa, sai 'yarsa ta ci gādonsa. 9Idan kuwa ba shi da 'ya, sai a ba 'yan'uwansa gādonsa. 10Idan kuma ba shi da 'yan'uwa, sai a ba 'yan'uwan mahaifinsa gādonsa. 11Idan kuma ba shi da su, sai a ba danginsa na kusa su mallaka, wannan zai zama umarni da ka'ida ga Isra'ilawa kamar yadda ni, Ubangiji na umarce ka.’ ”
An Zaɓi Joshuwa ya Gāji Musa
(M.Sh 31.1-8)
12 # M.Sh 3.23-27; 32.48-52 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Hau bisa kan Dutsen Abarim, ka dubi ƙasa wadda na ba Isra'ilawa. 13Bayan da ka gan ta, za ka mutu kamar yadda Haruna ya yi, 14domin ba ku yi biyayya da umarnina ba a jejin Zin. Lokacin da dukan jama'a suka yi mini gunaguni a Meriba, ba ku nuna ikona mai tsarki a gabansu ba.” (Wannan shi ne ruwan Meriba na Kadesh a jejin Zin.)
15Musa kuwa ya ce wa Ubangiji, 16“Bari Ubangiji Allah na ruhohin dukan 'yan adam ya shugabantar da mutum a kan taron jama'ar, 17#1Sar 22.17; Eze 34.5; Mat 9.36; Mar 6.34mutumin da zai shugabance su cikin yaƙi, don kada taron jama'ar Ubangiji su zama kamar tumakin da ba su da makiyaya.”
18 # Fit 24.13 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki Joshuwa, ɗan Nun, mutumin da ya dace, ka ɗibiya masa hannuwanka, 19ka sa shi ya tsaya a gaban Ele'azara, firist, da gaban dukan taron, sa'an nan ka keɓe shi a gabansu. 20Ka danƙa masa ikonka don taron jama'ar Isra'ila su yi masa biyayya. 21#Fit 28.30; 1Sam 14.41; 28.6Zai dogara ga Ele'azara, firist, don ya san nufina, ta wurin amfani da Urim da Tummin. Ta haka ne Ele'azara zai bi da Joshuwa da dukan taron jama'ar Isra'ila cikin al'amuransu.” 22Musa kuwa ya yi kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya ɗauki Joshuwa, ya sa shi ya tsaya a gaban Ele'azara, firist, da gaban dukan taron. 23#M.Sh 31.23Ya ɗibiya hannuwansa a kansa, ya keɓe shi kamar yadda Ubangiji ya umarta.

Currently Selected:

L.Ƙid 27: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

Video for L.Ƙid 27